CORONAVIRUS: Buhari ya nemi hadin kan kasashe don shawo kan cutar

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa da hadin kan kasashe ne kadai za a iya dakile barnar da cutar Coronavirus ta yi a duniya. Sannan kuma ya sha alwashin a Najeriya za a ci gaba da zakulo masu cutar tare da yin gwaji da killacewa, musamman a cikin al’ummar garuruwa daban-daban.

Buhari wanda ya yi bayanin a taron kai-tsaye ta bidiyo daga gida da Kungiyar Kasashe ‘Yan Ba Ruwan Mu suka gudanar a ranar Litinin, ya ce akwai matukar bukata kasashe a rukunin Yanki da Nashiya da Duniya baki daya su tashi su tsara hanya sahihiya domin ceto al’umma daga mummunar barnar da Coronavirus ta yi musu, ta hanyar karya musu tagomashin rayuwa, tattalim arziki da kuma jefa su cikin mummunan halin kunci.

Buhari ya ce, “Tun farkon barkewar cutar, kasashe da dama sun yi matukar kokarin ganin ba su bari cutar ta yadu a cikin kasashen da ke makautaka da su ba. Kuma su na kan kokarin ganin su na kulawa da wadanda suka kamu a cikin kasashen na su.

Buhari ya ce Najeriya ta yi rarar gani wajen rufe dukkan kan iyakookin ta da kuma hana jiragen sama da na ruwa sauka da tashi daga kasashe ko zuwa kasashe.

Ya ce an tashi haikan aka rika kafa cibiyoyin gwaji a wurare ko jihohi daban-daban.

“Mun kuma kuma gaggauta bayar da tallafin kayan abinci da kayan asibiti da agaji na kudade ga marasa galihu su milyan 3.6. Kuma an bada lamuni ga kasanan masu sana’o’i da matsakaitan su.” Inji Buhari.

A taron wanda sususan aka shirya da niyyar tattauna yadda za a shawo kan illar da Coronavirus ta yi,
Buhari ya gode wa Shugaban Azarbaijan, Ilham Aliyev, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Kasashe ‘Yan Ba Ruwan mu.

Share.

game da Author