Ministan Abuja Musa Bello ya bayyana cewa an kara kwana daya, yanzu kwanaki uku da mutane za su rika zuwa kasuwanni a babban birnin tarayya Abuja domin yin cefene.
Sanarwar ya biyo bayan ganawa da ministan yayi da kwamitin dakile yaduwar Korona a babban birnin Tarayyan.
An yanke cewa;
1 – Daga yanzu za a rika cin kasuwanni a ranakun Litinin, Laraba da Asabar daga karfe 8-3 na yamma
2 – Masu sai da kayan gona, maganin kwari, iri na shuka, da takin gona.
3 – masu saida Kayan gine-gine za su rika fitowa suna kasuwa.
4 – Haka kuma Kayan wuta musamman na gine-gine
5 – Wuraren saida kayan abinci dake cikin gari da aka hana su bude shaguna duk yanzu zasu rika hada-hada a kullum.
Duk kasuwannin da aka amince su bude, su tabbata sun yi feshi a wuraren sana’arsu sannan kuma su kiyaye dokokin hana cinkoso da gwamnati ta saka.