CORONAVIRUS: An gano Almajiri da mutumin da suka arce daga Inda aka killace su a Bauchi

0

Jami’an kiwon lafiya da jami’an tsaro a jihar Bauchi sun bazama neman wasu mutane biyu da aka auna kuma aka same sun kamu da cutar Coronavirus, Amma kuma suka sulale daga inda aka killace su, suka arce, ba a san inda suka yi ba.

Wani matashi mai shekaru 25 da aka kwantar a asibitin Abubakar Tafawa Balewa da wani almajiri mai shekaru 12 da aka dawo da shi daga jihar Kano ne suka tsere.

Shugaban Hukumar NPHCDA na jihar Rilwan Mohammed ne ya tabbatar da haka.

Mohammed ya kuma shaida cewa an gano almajirin tun a ranar da ya gudu sannan har yanzu ana neman dayan matashin.

“A binciken da muka yi mun gano cewa almajirin ya koma gida ne wajen iyayensa a garin Dass.

“Mun Sanar da sarkin Dass abin dake faruwa kafin nan muka aika da jami’an kiwon lafiya su dawo da shi.

Bayan haka Mohammed ya ce Bincike ya nuna cewa dayan matashin daya gudu ya na nan a kauyen Konkiyel dake karamar hukumar Darazo.

Ya ce a yanzu haka ‘yan sanda da jami’an tsaro na SSS sun san inda wannan matashi yake.

“Mun samarwa jami’an tsaro kayan samun kariya daga kamuwa da cutar domin su je su dawo da shi a killace shi.

A yanzu dai mutum 102 ne suka kamu da cutar a jihar.

Share.

game da Author