Shugaban hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya koka kan karancin wuraren killace wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar na inda ya ce akwai yiwuwar za a fara kwantar da mutane a gidajen su na kawai ba sai an kawo su asibiti ba.
Ya fadi haka ne a zaman da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar Covid-19 ta yi a Abuja a ranar Alhamis.
Ya ce a yanzu haka karancin wuraren killace mutane a duba su a Legar, Kano da Abuja ya na ci musu tuwo a kwarya.
Ihekweazu ya ce akwai gadajen kwantar da wadanda suka kamu da cutar 3,500 a kasar nan amma a yanzu haka samun wurin kwantar da mara lafiya a jihar Legas ya fara zama matsala.
Sannan kuma hukumar NCDC ta ce za ta ci gaba da aiki da gwamnatin jihar Legas domin ganin an kawo kasashen wannan matsalar.
Tun da cutar Covid-19 ta bullo a kasar nan ranar Alhamis ne ranar da kasar ta samu mutum sama 200 da suka kamu da cutar a rana daya.
Sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis ya nuna cewa an samu mutum 206 da suka kamu da cutar a Najeriya.
Mutum 1932 ne suka kamu da cutar, an sallami 319 sannan 58 sun mutu.
MATAKIN DA HUKUMAR TA DAUKA
Ihekweazu ya ce NCDC ta ce za a fara kula da wadanda suka kamu da cutar a gidajen su ne kawai. Sai dai ba kowa bane za a bashi damar a killace shi a gida.
” Za mu bincika mu gani idan mutum na da daki da gado shike nan kawai za a barshi a gida ne sai dai arika zuwa ana bashi magani.
Bayan haka ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya yi kira ga ‘yan Najeriya dake da Otel da gidajen da basa amfani da su, su bada aron su domin a samu isassun wuraren kwantar da wadanda basu da lafiya.
Ehanire ya ce NCDC ta hada hannu da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (NPHCDA) domin kara yawan asibitocin kula da wadanda suka kamu da cutar da karin yawan ma’aikata kuma.
Ya kuma ce za a horas da duba gari da ma’aikatan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko kan hanyoyin gano alamun cutar a jikin mutum domin yi masa gwajin cutar.
Discussion about this post