Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ana tunanin fara shirye-shiryen sake bude makaratun kasar nan, amma kuma ba gaba daya za a koma ba.
Da yake karin bayani a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Laraba, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa ana tunanin daliban da za su rubuta jarabawa ko wadanda suka fara rubuta jarabawa kafin a kulle makarantu ne za su fara komawa.
Sannan kuma ya kara da cewa dama ana fama da dimbin yaran da ke gararamba kan titi ba su zuwa makaranta.
To kuma Coronavirus ta tilasta rufe makarantu, hakan da ya haifar da zaman dukkan daliban kasar nan a gida.
“Duk da dai har yau ba a yanke shawarar ranar da za a koma ba, to ana shirye-shiryen raba daliban idan an koma. Wasu za su rika zuwa da safe, wasu kuma da rana, domin saukake cinkoso da kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus.”
Komawar Dalibai A Yanzu Ganganci Ne -Ministan Ilmi
Karamin Ministan Ilmi, Emeka Nwojuibi, ya bayyana cewa ganganci ne muraran idan aka ce a yanzu za a kwashi dalibai a ce kowa ya koma makaranta, a wannan hali da ake ciki.
Da ya ke jawabi bayan Boss Mustapha ya yi nasa, Nwojuibi ya ce har yanzu ba a sa ranar komawar dalibai ba tukunna.
Sannan kuma ya ce Ma’aikatar Ilmi ba za ta yi gangancin bude makarantu a yanzu ba, har sai ta samu tabbaci daga Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya cewa lokacin sake bude makarantun ya yi tukunna.
Sai dai shi din ma ya kara jaddada cewa ba lokaci daya za a koma ba. Kuma idan an koma din ma, to tilas za a bijiro da ka’idojin kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus a makarantu.
Discussion about this post