CORONAVIRUS: Access Bank zai rage albashin ma’aikata, maimakon sallamar wasu

0

Bankin Access, wanda ya bai wa gwamnatin tarayya tallafin naira bilyan daya, ya bayyana cewa zai rage albashin ma’aikatan sa, maimakon ya kafci wasu masu yawa ya sallama.

Wasu jami’an da suka tattauna batun rage albashin, sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa sun zartas da amimcewar rage albashin.

Wani babban jami’in bankin da bai so a ambaci sunan sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “Access Bank ya yanke shawarar zabtare albashin ma’aikatan, maimakon a kori ko a sallami wasu ma’aikatan bankin.”

“Nan da mako daya mai zuwa za ka ga ana ta sallamar ma’aikata. To mu a Access Bank, sai muka ce da a sallame ka da a rage maka albashi, wane ya fi dama-dama!”

Idan sai harkoki ba su dawo yadda su ke ba, to daga albashin watan Mayu za a fara yanke wa ma’aikatan bankin albashin su.

PREMIUM TIMES ta kalli wani bidiyo wanda Shugaban Access Bank, Herbert Wigwe ya ke wa wasu ma’aikatan bankin jawabi a wani taro, inda ya shaida musu cewa, “wadanda za a rage wa albashin za su kai kashi 75 bisa 100 na ilahirin ma’aikatan bankin a fadin kasar nan.”

“Saboda a yanzu ba mu bukatar jami’an tsaron da muka dauka aiki. Domin wadansu rassan bankin na mu ba za a bude su ba sai cikin Disamba. Ba mu bukatar dukkan ‘yan matan kwalisa masu raba wa manyan ma’aikata shayi. Ba mu bukatar dukkan masu shara da goge-goge da sauran ma’aikatan da aikin su bai wani taka kara ya karya ba.” Inji Wigwe.

“Ni ne wannan ragin albashin zai fi shafa, domin za a rage min kimanin kashi 40 bisa 100 na albashi na. Sannan ta gangaro kan sauran mukarrabai na, kowa a rage masa bisa auna yawan abin da ya ke dauka. Wannan shi ne batu.”

Idan za a biya tunawa, a farkon wannan shekarar ce bankin ya bayyana cewa ya yi cinikin zunzurutun kudi naira bilyan 666.75 daga watan Janairu zuwa Disamba, 2019.

Access Bank ya samu riba ta sama da naira bilyan 111 a 2019. Bayan bankin ya ware adadin harajin da ya biya, ribar da ya samu ta tashi naira bilyan 97.51.

Share.

game da Author