Najeriya bata taba samun yawan mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus kamar yadda alkalumman ranar litinin ya nuna.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar na ranar Lititin, akalla mutm 245 nme suka kamu da cutar a Najeriya. Sannan kuma idan ba a manta ba a wannan rana ne aka yardar wa jama’a su fara fita domin ci gaba da harkokin su a jihohin Ogun, Legas da babban birnin tarayya, Abuja.
Wannan alkalumma ya tada wa mutane da dama hankali ganin cewa a lokacin da ake samun yawa-yawan mutane sun kamu da cutar ne ita kuma gwamnati ke sassauta dokan zaman gida dole.
Mutum 245 ne suka kamu da cutar a rahotan NCDC da ta fitar Litinin.
A ranar 4 ga watan Mayu, jihohin Legas, Katsina da Kano ne suka samu yawan mutanen da samfarin su ya nuna sun kamu da cutar.
Zuwa yanzu an yi wa mutane 18,536 gwajin cutar Coronavirus a Najeriya. Mutum 2802 ne suka kamu da cutar zuwa ranar litinin 4 ga watan Mayu.
Har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya.
Mutum 1,183 suka kamu da cutar a jihar Legas, Sai jihar Kano da ke bi mata da mutum 365, FCT – 297, Borno – 100, Gombe – 96, Kaduna – 81, Ogun – 85, Bauchi – 80, Sokoto – 66, Edo – 62, Katsina – 83, Osun – 37, Oyo and Jigawa – 39, Delta – 17, Kwara and Akwa Ibom – 16, Rivers – 14, Yobe, Zamfara and Ondo – 13, Ekiti, Adamawa, Kebbi – 13,Nasarawa – 11, Enugu and Taraba – 8, Ebonyi and Bayelsa – 5, Plateau – 3, Niger – 4, Imo, Benue and Abia – 2.
Discussion about this post