Buhari ya karbi jikon maganin Korona daga Madagaska

0

Shugaban Kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, ya mika wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari kason kyautar jikon maganin Korona da kasar Madagaska ta rabawa kasashen Afrika.

Shugaban Kasar Guinea, Embalo ya shaida wa Buhari cewa kasar Madagaska ta ce raba wa kasashen Afrika wannan siddabaro nata domin ko za a iya amfani da shi wajen warkar da masu fama da cutar Korona a kasahen mu.

Bayan haka ya ce yayai amfani da wannan dama domin ya ziyarci shugaba Buhari wadda kamar mahaifi yake a wurinsa domin ya bashi shawarar yadda zai tafiyar da mulkin kasar sa sannan kuma yasa masa albarka.

” Shugaba buhari kamar mahaifine a wuri na, ni kuma dan sa ne. Na zo Najeriya domin in gana da shi kuma ya saka mi alabarka, bayan nasarar da na samu a zaben kasar guinea.

A nashi jawabin shugaba Buhari ya ce ba zai sa a fara amfani da wannan magani na madagaska a kasar nan ba sai an yi binciken kimiyya a kai tukunna an kuma tabbatar da ingacin maganin.

” Ba zan sa a fara amfani da maganin madagaska ba sai an yi gwajin kimiyya a kai. Kwararru za su buba ingancin wannan magani kafin nanan za mu dauki matsaya, ko muyi amfani da shi ko kuma mu hakura.

Sannan kuma ya godewa shugaba Embalo bisa ziyarar da ya kawo masa yana maicewa Najeriya zata ci gaba da mara wa kasar Guinea baya.

A karshe kuma ya jinjina wa shugaban kungiyar ECOWAS, Mamoudou Yusoufu na kasar nijar bisa yadda yake jagorantar kungiyar.

Share.

game da Author