Boko Haram sun tarwatse sun dai-daice a dajin Sambisa – Enenche

0

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa Boko Haram sun tarwatse a cikin dajin Sambisa kowa ya kama gaban sa.

Kodinatan yada Labaran rundunar Sojin, John Enenche ya bayyana cewa a dalilin luguden wuta da suka rika sha a maboyan su dake dajin Sambisa, yanzu mayakan boko haram din duk sun tarwatse sun dai-dai ce a dajin.

John Enenche ya kara da cewa a yanzu haka sun samu bayannan sirri cewa Boko haram suna sake sabon shiri domin afkawa sansanoni da barikin sojoji dake yankin da kuma kai wa mutanen gari hari.

” Sojin sama za su ci gaba da yi musu luguden wuta ta sama babu kakkautawa sannan dakarun mu na kasa kuma suna bi suna kakkabewa. Boko Haram fa yanzu sun shiga uku.

” Daga yanzu madarar luguden wuta za su rika kwankwada babu kakkautawa sai mun kakkabe su tas a yankin Arewa Maso Gabas. Kai ba ma su ba duk wani dan ta’adda ya kade da sojojin Najeriya. Za mu bisu har inda suka mu diran musu ta sama da kasa, sai mun gama da su.”

Share.

game da Author