BOKO HARAM: Mun kashe ‘yan ta’adda 135 a jihar Barno – Hukumar Sojoji

0

Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta bayyana cewa zaratan sojojin ta sun kashe Boko Haram da ISWAP har 135 a wasu raraka da ragargaza da suka yi wa ‘yan ta’addar a Jihar Barno.

Babban Jami’in Sadarwa na Kasa, John Enenche ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja, inda ya ce a yayin fatattakar ‘yan ta’addar, an kuma kama mutane 16 masu yi musu leken-asiri.

Ya ce zaratan yankin ‘Operation Kantana Jimla da ke wani bangare na ‘Operation Lafiya Dole’ ne suka yi gumurzun samun wannan babbar nasara.

Ya ce wannan nasara sun dauke ta matsayin wani gagarimin aikin share Boko Haram da ISWAP a yankin da ya ce kusan daga shi babu sauran wani aiki a gaban sojojin sai fadan karshe, wanda a lokacin ne za su karasa fatattakar ‘yan ta’adda gaba daya daga Najeriya.

Ehenche ya ce Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ne da kan sa ya tsara dabarun yadda aka samu wannan gagarimar nasara kan Boko Haram.

Ya kara da cewa a yanzu dan burbushin Boko Haram da suka rage duk sun rude sun gigice sun tarwatse.

“Ranar 1 da 2 Ga Mayu an kashe Boko Haram 78 a wani harin da aka kai musu ta sama a Timbuktu. Sannan kuma a Buk da ke cikin Karamar Hukumar Damboa an kashe wasu 56 kuma aka kama masu leken-asiri su 16.

Tun cikin watan Afrilu ne sojojin Najeriya suka bayyana cewa sun fara arangamar da ba za su tsagaita na har sai sun kakkabe Boko Haram rankatakaf.

Janar Buratai ya dade a Arewa maso Gabas inda ya ke bi ya na tsare-tsaren yakin karasa murkushe Boko Haram.

Share.

game da Author