BAUCHI: Ba a yi min hudubar akwai saduwa a aure ba, shi yasa da mijina ya bukace ni na kashe shi – Salma

0

Salma Hassan, ‘yar shekara 18, ta bayyana wa ‘yan sanda cewa ta kashe mijin ta da wuka saboda bata san akwai harkar saduwa da juna a aure ba.

Ita dai Salma ta kashe mijinta ne a lokacin da ya tunkare ta domin saduwa da ita a matsayin matar sa.

” Ni ba a taba yi min hudubar cewa idan nayi aure zan sadu da mijina ba. Da mijina Mustapha ya nemi ya sadu da ni sai na yi zaton zai yi min fyade ne da karfin tsiya. Daga nan sai na rarumi sharbebiyar wuka don in kora shi.

” Ya ki biye min shi kuwa sai ya ci gaba da nufo ni, ni kuma na caka mai wukar a kokor zuciya.

Salma tace bayan ta ki bashi hadin kai sai mijinta mai suna Mustapha ya hauta da duka. Ya dinga kilanta har ya kai ga ta aikata kisan.

Salma ta aikata wannan mummunar abu ne a Itas-Gadau.

Mustafa ya rasu bayan an kai shi asibiti a Itas-Gadau, amma kafin a natsa har a iya duba shi rai yayi halin sa.

Share.

game da Author