Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce bai shiga siyasa don ya warware matsalolin Najeriya ba.
Amaechi wanda siyasa ta aura kuma ya ke rike da mukamai tun daga 1999 har yau, ya ce matsalar rashin aiki yi da zaman-banza ne su ka sa ya shiga siyasa tun farko.
“Ni ba hadamar mulki ko shugabanci ko kishin warware matsalar Najeriya su ka sa na shiga siyasa ba. Na shiga siyasa saboda matsalar rashin aikin yi ne.”
Haka aka ruwaito shi ya furta a cikin wata tattaunawa da jaridar Punch ta yi da shi.
Amaechi ya fara katari da siyasa cikin 1999, inda aka zabe shi dan Majalisar Dokokin Jihar Rivers daga nan kuma ya zama Kakakin Majalisar Jiha. An sake zaben sa cikin 2003, duk a karkashin PDP.
Ya tsaya takarar zaben fidda-gwanin zaben gwamna a karkashin PDP na jihar Rivers. Ya fadi zaben, Celestine Omeiha ya ci zaben Gwamna, Amaechi ya kai kara, kotu ta ba shi nasara.
Ya yi Gwamna sau biyu, amma cikin 2013 ya fice daga PDP ya koma bangaren Buhari suka kafa APC. Ya taka rawa sosai a nasarar Buhari a zaben 2015. Shi ne ma Daraktan Kamfen na Buhari.
A yanzu shi ne Ministan Sufuri, mukamin da ya ke rike tun 2015.
A hirar da aka yi da shi, ya ce har yau talaka bai samu kyakkyawan wakilci a gwamnati ba, ko ta yanzu ko kuma gwamnatocin baya.
” Har yanzu dai talaka na nan inda ya ke. Kuma da wahalar gaske a iya kawar masa da wannan talaucin.”
Sai dai kuma idan ba a manta ba, Amaechi ya taba amfani da karfin ikon ofishin sa, ya karkatar da gurabun karo ilmi kyauta da kamfanin CCECC ya bayar da ‘ya’yan masara galihu, amma duk Amaechi ya rabas da gurabun ga ‘ya’yan masu mulkin kasar nan.
Da ya koma kan batun yadda aka bar matasa a baya wajen raba mukamai a mulkin kasar nan, ya ce matasa sai fa sun tashi tsaya an rika gogayya da su. Ba wai kwanciya kawai za su yi su na ta addu’a ba.
Ya ce ita siyasa romon jaba ce, ” Sai ka tashi da mutum ku na kwanciya a kan gado daya. Amma da ya samu damar siyasa, ka kan ka zai fara.”