Atiku ya rage ma’aikata 51 a Radiyo da Talbijin na Gotel

0

Akalla ma’aikatan Gotel Communications Limited, da ke Yola, mai Radiyo Gotel da Gotel Television, mallakar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar aka sallama daga aiki.

Idan ba a manta ba, cikin 2016 Gotel ya yi wa dimbin ma’aikata kakkabar ‘ya’yan kadanya, daga nan kuma aka sabunta yarjejeniyar sake daukar burbushin wadanda suka rage.

A wannan makon kuma said Gotel ya sake kamfatar ma’aikata 51 ya sallama daga aiki.

Ma’aikatan wadanda dama na wucin-gadi ne a gidajen radiyo da talbijin din na Gotel, sun ce, “ba a ba mu dalilin korar ta mu da aka yi ba.”

Wani da abin ya shafa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba a ce musu ga dalili ba. Amma dai ya na ganin cewa an sallame su ne saboda Atiku kwanan baya ya hade kamfanonin sa gaba daya a wuri guda, yanzu sun koma Priam Group.

Ya ce Priam Group ne zai ci gaba da tafiyar da gaba daya harkokin kasuwanci da hada-hadar Atiku, a karkashin Hukumar Gudanarwa daya tilo.

Majiya ta ce tuni Atiku ya dauko wasu Indiyawa wadanda a yanzu su ne ke kula da harkokin gudanarwar Priam Group.

Martanin Gotel: PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Shugaban Gotel Communications, Elyakub wanda ya kara tabbatar masa da sallamar ma’aikatan, kuma ya ce hakan ya faru ne saboda sabon tsarin tattara harkokin gudanarwar hada-hadar kamdanonin Atiku a wuri daya.

Ya kuma tabbatar da cewa a yanzu ana gudanar da komai a karkashin Priam Group ne.

Wasu ma’aikatan da suka ce an dauke su aiki a wa’adin shekara biyar, a yanzu ne ma suka cika shekara biyu da rabi da fara aikin, amma aka sallame su.

Share.

game da Author