Anya Buhari bai yi gaggawar janye dokar hana walwala a jihohin Legas da Abuja ba Kuwa?
Tun lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya janye dokar Zaman Gida Dole da ya saka a Jihohin Legas, Ogun da Babban Birnin Tarayya Abuja, na fada cikin tunani mai zurfi ganin cewa dalilin da ya sa aka saka wannan doka wacce yaduwar annobar Coronavirus ba ta kau ba kuma ma annobar kara yaduwa take a wadannan jihohi da kasa baki daya.
Annobar Coronavirus ta karade Najeriya yanzu, domin a kullum sai an samu karin mutum da dama da suka kamu da cutar. Abin ya zama tashin hankali ga wadadanda suka san ciwon kansu a Kasar nan.
Abin dake ci wa mutane da dama tuwo a kwarya kuma shine yadda har yanzu wasu mutane da dama basu yadda cewa akwai ma cutar ba. Karin mutane da ake samu da kuma mutuwa da a kullum ake yi sanadiyyar cutar bai dada su da kasa ba, gani suke abar su kawai su ci gaba da gwamutsuwa.
Jihar Kano da yanzu itace ke neman zama cibiyar yaduwar cutar a Najeriya, abin ya na neman ya gagari hatta gwamnati ne da mahukunta. A cikin wannan mako wasu masu dauke da cutar suka garkame wasu likitocin dake duba su. Baya ga kamuwa da liktocin ke yi da cutar a jihar.
Sannan kuma wai duka a Najeriya za ka ga wasu na waske wa daga inda aka killace su a neme su a rasa, wannan abu da me yayi kama, saboda Allah.
Dokar a rika nesa-nesa da juna bai yi tasiri ba kwata-kwata, kowa gwamutuwarsa yake abinsa.
Baya ga mace-mace da aka rika samu da dama, daruruwan Almajirai duk sun kamu da cutar. Rahotanni da muka rika karantawa sune ma suka baza cutar a jihohin arewa da dama.
Amma kuma har yanzu yana neman yaza kawai mutane suna sio a rabu dasu su ci gaba da harkokin su ne, idan an mutu shikenan idan kuma an rayu shikenan.
Duk da rahotannin da aka rika samu na dubban mutane da suka mutu a kasashen duniya, har da ‘yan Najeriya dake zaune acan wannan bai tsorata yan Najeriya ba. Masallatai a kasar Saudiyya duk an rufe su amma duk bai tsorata dan Najeriya ba.