Mata masu ciki sun koka kan yadda annobar Korona ta hana su zuwa asibiti yin awon ciki da ganin likita kamar yadda ya suka saba.
Matan sun ce ma’aikatan asibiti sun wmarci duk mace mai ciki za ta iya zuwa asibiti domin ganin likita idan tana da matsalar da cikin da take dauke da shi ne kawai.
Ma’aikatan asibitin sun kuma bai wa kowace mace lokaci da ranakun da za ta iya zuwa ganin likita idan ta samu matsala da cikinta.
Amarachi Moses ta ce ta yi rajistan awon a babban asibitin Kubuwa dake Abuja inda likitocin sun hana duk mata masu ciki zuwa asibiti sai lokacin haihuwa.
Amarachi ta ce da taimakon mijinta tana motsa jikin ta iya gwargwado a gida yanayin zaman gida dole.
Bayan haka mata masu ciki sun koka da yadda kayan haihuwa da jarirai ke da tafka dan karan tsada a kasuwanni yanzu.
Fatima Musa daga Kaduna ta ce a dalilin rufe kasuwanni da gwamnati ta yi domin dakile yaduwar cutar Korona kayan jarirai da na haihuwa da suka saba siya da arha an tsawwala musu kudi sannan wasu lokutan ma ba a samun wasu a kasuwannin.
Wata mata mai suna Olayinka Kolawole ta ce har yanzu ta kasa kammala siyan kayan jaridar da na haihuwa da ya kamata saboda tsadan kayan a kasuwa.
Olayinka ta ce akwai ranar da ta je kasuwa da Naira 20,000 amma ta rasa abin da ta siya da kudin.
Ta ce duk hakan ya faru ne saboda gudun rashin samun kayan a kasuwa.
Ijeoma Owecha da ta haihu a asibitin ‘Nigerian Air Force NAF’ ta ce hankalin ta ya tashi a ranar da ta ji cewa asibitin za ta bude sashen kula da masu fama da cutar Covid-19.
Ta ce jin haka ya sa ta bukaci a sallame ta daga asibitin domin gudun kada Ita ko kuma jaririnta su kamu da cutar.
Ijeoma ta ce daga yanzu ta yarda ta rika zuwa cibiyar kiwon lafiya na matakin farko dake garki domin guje wa kamuwa da cutar.
Likitan mata Oliver Ezechi ya ce kare mata masu ciki a wannan lokaci da cutar Covid-19 ta addabi mutane na da muhimmancin gaske a kasar nan.
Ezechi ya ce a dalilin haka ne ya sa suka dauki wasu matakai da za su taimaka wajen kare kiwon lafiyar mata da hana yaduwar cutar.
Ya ce wadannan matakai sun hada da rashin tara mata wuri daya a lokacin da suka zo awon ciki.
Discussion about this post