‘Yan jagaliya sun tirsasa wani fasto yin wanka a cikin kwata, bayan an zabga masa bulala har sau 35.
An yi wa faston wannan wulakanci ne bayan an zarge shi da sukar Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Ebonyi.
Mai wa’azin, mai suna Chukwu Obeni, an ce ya rubuta labarin da ba gaskiya ba a shafin sa na ‘Facebook a kan Oko Enyim, Shugaban Karamar Hukumar Afikpo ta Arewa da ke Jihar Ebonyi.
Nuna wannan cin mutunci da aka yi wa mai wa’azin a been bidiyo da kuma hotunan, ya jawo jama’a da dama na yin tir da yadda ‘yan siyasa su ka maida kan su wasu Fir’aunonin da ba su jimirin a soki ra’ayin su.
Wani mai rajin kare hakkin jama’a mai suna Samson Nweke, ya ce shi da wasu ne suka dauki faston zuwa wani asibitin kudi, inda ya ke kwance a yanzu haka, ana duba lafiyar sa.
Bidiyon da aka nuna a twitter, an ga inda ake zabga masa bulalar doki har sau 35. Sannan kuma aka sa ya rika wanka da ruwan kwata, tsawon wasu ‘yan mintina.
Nweke ya ce za su bi wa faston hakkin sa daga wannan cin zarafi da aka yi masa.
Kakakin Yada Labarai ta ‘Yan Sandan Ebonyi, Loveth Odah, ta ce an kama mutum daya kuma ana bincike.
Ko cikin azumin nan a Jihar Kano Mahukuntan sun sa limami share kofar gidan sa, bayan an tsatstsala masa bulala, saboda karya dokar hana yin jam’i, don gudun kamuwa da Coronavirus.
Discussion about this post