An yi jana’izar tsohon gwamnan Sokoto Marigayi Garba Nadama a Sokoto

0

A ranar Talata ne jikan tsohon gwamnan jihar Sokoto, Imran Ahmed-Rufai ya tabbatar wa PREMIUM TIMES rasuwar kakan sa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Garba Nadama.

Marigayi Garba Nadama ya rasu yana da shekaru 82 a duniya a gidan sa dake Sokoto ranar Litinin.

Marigayi Nadama ya dare kujerar gwamnan jihar Sokoto a 1982 bayan rasuwar Shehu Kangiwa. Sai dai bai dade a mulki ba, shekara da dal, sai sojoji suka yi juyin mulki, wadda Buhari ya zama shugaban Kasa.

Bayan haka ya shiga siyaya sannan ya rike mukamai na siyasa da mamban kwamiti na musamman na jam’iyyar PDP. Sannan a lokacin mulkin sa ne aka kirkiro da Kwalejin kimiyya da Fasaha dake Kauran Namoda.

Allah ya ji kan sa Amin.

Share.

game da Author