An sallami ma’aikatan lafiya 40 da suka kamu da Korona daga asibiti a Kano

0

Babban Asibitin Aminu Kano ta sallami likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya 40 da suka warke daga cutar Korona

Likitoci da ma’aikatar kiwon lafiya 50 ne suka kamu da cutar kuma an kwantar da su a asibitin Aminu Kano domin samun kula.

Shugaban asibitin Abdurrahman Sheshe ya Sanar da haka ranar Alhamis da yake karbar gudunmawar kayan aiki da kamfanin magani na ‘Orange Drugs Limited’a asibitin.

“Daga cikin ma’aikatan kiwon lafiya 50 dake kwance a asibitin Aminu Kano 40 sun warke daga cutar Korona, 10 na samun saukikuma babu wanda ya rasu a cikin su.

Sheshe ya ce ana sa ran cewa za a sallami sauran ma’aikatan lafiya 10 din da suka rage kafin karamar Sallah.

Idan ba manta ba a kwanakin baya ne PREMIUMTIMES ta bada labarai yadda ma’aikatar lafiya suka kamu da cutar Covid-19 a lokacin da suke kula da masu fama da cutar a asibitocin jihar.

Yanzu haka mutum 847 ne suka kamu cutar a jihar.

Share.

game da Author