ALMAJIRCI: Yadda Gwamnonin Arewa suka tashi haikan domin hana kai yara garuruwa karatun allo da barace-barace

0

Idan ka na so ka fahimci irin matsananciyar yunwar da ke tattare da irin wadannan kananan yara masu bara da dan kwano, to ka je wurin sayar da abinci ko kasuwa ka ga abin tausayi.

Da zaran ka sayi abinci, ka na zaunawa za ka fara ci, sai almajiri kamar uku zuwa biyar su kewaye ka. Su koma gefe, su kura maka ido. Idon su na kallon hannun sa lokacin da za ka yanko lomar tuwo, kuma haka za su bi ka da kallo, har lokacin da za ka kai wannan lomar a baki. Wasu ma har lissafa ko loma nawa ka yi za su yi.

Haka wani zai ji tausayin su, ya dauki wanda ya rage, ya mika musu. Wani kuma haushi zai kama shi, ya dauka ya ba su, amma ba don ya koshi ba.

Duk da cewa dukkan garuruwan Arewa ko’ina ka je haka za ka gani, amma abin da wakilin mu ya gani a Daura, mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari, ta tayar masa da hankali. Daura gari ne na ma’aikatan gwamnati, ‘yan kasuwa, ‘yan gayu da tsoffin ma’aikatan gwamnati, ciki kuwa har da tsohon Shugaban Kasa, kuma Shugaba a yanzu, Muhammadu Buhari.

Haka rukunonin wadannan mutane ke wucewa a kullum su na ganin irin wadannan dandazon almajirai su na bara sanye da kaya kodaddu, yagaggu, farkakku, dakun-dakun kuma ga datti a jiki.

Almajirci: ‘Buzuzu Ma Nama Ne’

Da dare, lokacin da kowa ke kwance gida ya na shirin cin abinci, a lokacin ne kuma hankalin almajiri ke tashi ya shiga fagamniyar neman abin da zai ci. Kuma duk abin da zai nema, bai wuce abin da maigida, matar gida ko yaran gida su ka ci suka rage ba.

“Ko dan dago-dago,
Ko dan tsaki-tsaki,
Iya ko dan kanzo,
Iya ko guntun gaya ne,
Ko kun ci kun rage,
Ko sauran yara ne!”

A gidan da almajiri ya yi sa’a ne za a ba shi sauran da yara suka ci suka rage, bayan an yi jagwalgwalo da abincin. Zai karba ya ce “Allah ya saka da alheri.” Shi ya na ganin an yi masa aikin samun lada a wurin Allah Madaukaki. Shi maai bayar da jagwalgwalon sauran tuwon na ganin cewa aikin samun lada a wajen Allah ya yi.

A haka wasu ke samu su ci su koshi, har su yi guzirin da za su kai wa malamin su, shi ma ya ci.

Kokarin da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi ba fara kawar da barace-barace, inda ya kafa makarantun tsangayu masu yawa a kasar nan, ya ci tura, domin bayan tafiyar sa, gwamnonin Arewa sun watsar da shirin ya shiririce.

Jihar Kano ce ta fara aikin kakkabe almajirai ta na kwashe au ta na maidawa jihohin su na asali. Kuma kwamishinan Lafiya Mohammed Sanusi Kiru ya shaida dalilan kwashe almajiran ana mayar da su gida, musamman yanzu ganin yadda su kW a cunkushe cikin kazanta, yanayi wanda ya ce idan cutar Coronavirus ta shiga cikin su to shikenan, ta samu wurin zama.

Duk da yunkuri da kokarin da gwamnati ke yi wajen inganta ilmi ta cannon Tsarin Muradin Karni, wannan bai hana a samu yara masu gagaramba ba su zuwa makaranta har milyan 10. Haka Hukumar UNICEF ta bayyana, yawancin yaran kuma duk a Arewa su ke. A Arewar ma sun fi dandazo, kaka-gida da katutu a Bauchi, Neja, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, Kebbi, Gombe, Adamawa, Taraba da garuruwan da ke kewaye da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

UNESCO dai ta ce kashi 29 zuwa 35 bisa 100 na yaran Musulmai a Arewa, ana kai su almajirci ne, ba su samun damar karatun zamani, duk almajirci ake tura su.

Da yawan su kuma su kan watsar da karatun su kama sana’o’in hannu, ko aikatau a shaguna, gidaje ko kasuwanni.

Akan Samu Biloniya, Akan Samu Takadari

A yanzu haka a Kano akwai hamshakan attajirai wadanda za a iya samun biloniyoyi a cikin su, amma asalin au almajirai ne. A kan kuma yi rashin dace wani ya shiga duniya. Sai ya girma idan an binciki tarihi, sai a ce sanadiyyar almajirci ya baro garin su.

Ba Aliyu wani almajiri da wakilin mu ya ritsa a Sokoto ne kadai ba ya iya fassara maka ‘Suratil Fatihah’ ba. Ka je Argungu ko Kebbi. Ka je Katsina ko Kano. Ka je Bauchi ko Gusau. Kai duk inda ka karade a Arewa, har ka nausa kololuwar karatun allo a Maiduguri, yaran har saukar su karatu zar ake koya musu, ba sanin ma’anar abin da su ke koyo ba.

A halin yanzu Gwamnonin Arewa sun dauki haramar kwashe almajirai su na maida su garuruwan su saboda gudun fantsamar cutar Coronavirus a jihohin su. Jihar Kano ta fara, sai Kaduna ta zo ta kama, har ta zarce Kano, kamar yadda Gwamna Nasiru El-Rufai ya ce Kaduna ta kwashe almajirai 30,000, an maida su garuruwan iyayen su, kuma ba za a bari su sake kokawa ba.”

Ita ma Jihar Nasarawa tuni ta fara kwashe su ta na lodawa a mota zuwa jihohin su. Kuma jihar ta nuna nan gaba kadan za a kakkabe su karkaf daga kan titinan jihar.

Sai dai kuma Farfesa Jibrin Ibrahim na ganin ba wai kwashe almajirai ana maida su jihohin su ne kadai zai magance matsalar ba. Ya ce sai gwamnonin Arewa sun zauna sun fito da sahihan hanyoyin magance musabbin abin da ke sa a wannan zamani iyaye ke tura ‘ya’yan su makarantun allo yin almajirci.

“Saboda yanayin yadda su ke kwasar almajiran su na maidawa jihohin su a yanzu, kamar wata hobbasar ganin-ido ce saboda Coronavirus.”

Shi kuwa Kwamishinan Ilmin Jihar Bauchi, Aliyu Tilde, cewa ya yi, duk wani kokarin sake inganta karatun almajiran da ake dawo wa jihar da su, ya dogara ne bisa irin goyon baya da iyayen su za su bayar.

Karamin Ministan Ilmi, Chukwumeka Nwajube, ya ce, “yanzu dai wannan gwamnati ta damka tsari da makarantun tsangayu da gwamnatin Jonathan ta kirkiro a hannun gwamnoni.” Haka ya bayyana a ranar Alhamis.

Share.

game da Author