Akalla mutum miliyan 8.5 suka kurmance a Najeriya – Masana

0

Shugaban Kungiyar likitocin kunne ta Najeriya SPAAN, Julius Ademokoy ya bayyana cewa akalla mutum miliyan 8.5 sun kurmance a Najeriya.

Ademokoy wanda farfesa ne ya fadi haka a taron inganta jin magana da Kungiyar ta yi a cibiyar NUJ dake Ibadan ranar Alhamis ya ce SPAAN ta shirya Wannan taro ne da hadin gwuiwar cibiyar ‘Smile Train Incorporation’.

Ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukan matakan kare mutane rasa jin su saboda adadin yawan mutanen dake kurmancewa a kasar na dada yawa matuka.

“A shekaran 1999 mutum miliyan 7.3 ne suka rasa jin su a kasar nan sannan a yanzu haka adadin yawan mutanen ya karu zuwa miliyan 8.5.

A duniya yawan mutanen da suka kurmance sun kai miliyan 466.

Ademokoy ya ce Najeriya na bukatan karin kwararrun likitoci da za su taimaka wajen kare mutane daga kurmancewa a kasar nan.

“A yanzu haka akwai Kwararrun likitocin kunne kasa da 300 ne a kasar nan.

Ya ce a kullun rana mutane a kasar nan na fama da matsaloli dake kai wa su rasa jin su.

Wadannan matsaloli sun hada da ta’ammali da miyagun kwayoyi, yawan amfani da na’uran sauraron sauti wato ear pieace, yawan jin karan bindigogi da sauran su.

Ademokoy ya yi kira ga gwamnati da ta bude asibitin kunne da gyara furici a duk kananan hukumomin kasar nan domin duba masu fama da matsaloli irin haka.

Ya kuma ce kamata ya yi gwamnati ta saka darasin gyara furici a duk makarantu domin gyara yadda yara za su rika yin maganin idan sun fara girma.

Bayan haka mataimakin shugaban Kungiyar Oyedunni Arulogun ta ce kamata ya yi gwamnati ta wayar da kan mutane musamman na yankin karkara kan hanyoyin dake sa mutum kurmancewa.

Ta ce rashin cin abincin da ya kamata, ta’ammali da kwayoyi, yawan sauraron kara, yin amfani da abubuwa masu kaifi a kunne, jin rauni a kai ko a kunne da sauran su na daga cikin matsalolin dake kurmantar da mutum.

Jami’ar ‘Smile Train Incorporation’ Adeola Olusanya ta yi kira ga gwamnati da ta tilasta wa iyaye yi wa ‘ya’yan su gwajin jin magana da furici domin guje wa matsalar kurmancewa idan yaran sun girma.

Share.

game da Author