Kwamitin dakile yaduwar Cutar Coronavirus na Jihar Gombe Karkashin shugabancin Farfesa Idris Mohammed, ya yi takaicin zanga-zangar da wasu dake dauke da cutar suka yi a garin Kwadon, Karamar hukumar Yamaltu-Deba, Jihar Gombe.
Wannan kwamiti na so ya fayyace wa mutane komai domin a san ainihin abin da ya faru a wannan rana da abubuwan da suka faru a baya kafin wannan zanga-zanga.
Abin da ya faru shine daya daga cikin wadanda aka killace a wannan wuri ta na dauke rauni a jikinta da likitoci kan duba ta. Wata ‘yar uwar ta ta dage ita ba ta gamsu da maganin asibiti da ake yi wa ‘yar uwanta ba tana so a kyale ta su tafi kauye ayi mata na gargajiya.
Duk da cewa tana da daman kula da ‘yar uwanta a ko-ina, amma ba mu amince mata ba saboda tana dauke da Coronavirus.
Tuni dai har kwamitin, ya maida wannan mara lafiya can kauyen su, sannan an killace ta a inda ba za ta yada cutar ba.
Wadannan da aka killace duk sun dawo Gombe ne daga jihohin Legas, Kano da Abuja bayan an saka dokar hana walwala a wadannan Jihohi da babban birnin tarayya, kuma ma dai su ayyukan yau da kullum ne suka yi ko a can inda suke.
Da suka dawo mun ce dole sai an yi musu gwajin cutar, wadanda aka samu sun kamu da ita ne muka killace a wuraren da gwamnati ta tanada, sannan muka wadata su da abinci da kuma duk abinda za su bukata.
Sai dai kuma wasu daga cikin su suka fara cewa lallai gwamnati sai ta ciyar da ‘yan’uwan su suma tunda suna killace basu iya samar musu da taimako.
” Dama kuma gwamnan jihar ya kafa kwamitin raba tallafi ga talakawa da marasa karfi a jihar. Kuma tun kafin su yi wannan zanga-zanga, gwamnati ta fara tantance ‘yan uwan wadanda aka killace domin basu tallafi.
” Abin bakin ciki kuwa shine yadda mutanen garin suka gwamutsu da wadanda suka fito zanga-zangar, wannan abin tashin hankali ne matuka sannan kuma ya nuna cewa wasu har yanzu basu yarda annobar Coronavirus gaskiya bace.
A karshe Dr Mohammed Kwami na kwamitin dakile yaduwar COVID-19 na jihar yace kwamitin ya fara farautar wadanda suka yi cudanya da wadanda suka fito zanga-zanga domin yi musu gwajin cutar.
Sannan Kuma gwamnati zai ci gaba da kula da wadanda suka kamu da cutar a jihar da kuma dakile yaduwar cutar.