A soshiyal midiya mu ke ganin labaran masana, ‘yan-tsibbu da bokaye masu ikirarin gano maganin Coronavirus -NAFDAC

0

Shugabar Hukumar Kula Da Abinci Da Magunguna Ta Kasa (NAFDAC), Moji Adeyeye, ta bayyana cewa a soshiyal midiya da shafukan jaridu ne kadai ta ke ganin labarai na masu ikirarin cewa sun gano maganin gargajiya wanda zai warkar da cutar Coronavirus.

Adeyeye ta bayyana cewa har yau mutum daya ne tak ya tunkari hukumar NAFDAC ya nemi ta duba ingancin maganin da ya yi ikirarin cewa ya hada na gargajiya, da ya ce zai iya warkar da Coronavirus.

“Shi ma wancan mutum dayan, ba wai maganin cutar ce gidigat ya ce ya gano ba. Cewa ya yi ya gano maganin alamomin rashin lafiyar da ake ganin su ne alamomin kamuwa da cutar.

“Saboda haka mu da dai jin labarai ko gani a jaridu da soshiyal midiya, na wasu masana, ‘yan-tsibbu, bokaye da ke ikirarin samo maganin Coronavirus kawai. Ba su zuwa domin su nemi hukumar mu ta tantance ingancin su.”

Idan ba a manta ba, cikin wadanda suka yi ikirarin samo maganin, har da babban basarake, Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi ya yi ikirarin cewa ya gano maganin garganiya na sayun da ganyen itatuwa da ya ce duk karfin cutar Coronavirus, to maganin zai iya dagargazar da ita.

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ya bayyana cewa kada kuskura a jaraba wani maganin garganiya da nufin Coronavirus, har sai an gwada inganci da sahihancin sa tukunna.

Sannan kuma ya ce ba za a yi shisshigi ko kasassabar gwada maganin a jikin dan adam ba, sai dai a jikin dabba.

A karshe shugabar ta NAFDAC ta kara da cewa kwamitin inganta magungunan gargajiya da NAFDAC ta kafa, ya na taro da masana, masu kamfanonin hada magunguna da sauran masu ruwa da tsaki a harkar magani, domin a gano hanyoyi kuma a bunkasa inda magungunan gargajiya suka bambanta da na zamani.

Share.

game da Author