2011-2020: ‘Yan Najeriya sun biya diyyar naira bilyan 7 ga masu garkuwa da mutane

0

Yayin da aka wayi gari ta’asar garkuwa da mutane ta zama hanyar kudancewa a lokaci kankane ga manya da kananan masu aikata laifuka, wani rahoto ya bayyana irin asarar da ‘yan Najeriya suka tafka tsawon shekaru 9 a hannun masu garkuwa da mutane.

Rahoton da Cibiyar SB Morgan ta fitar a farkon watan Mayu, ya nuna cewa ‘yan Najeriya sun biya masu garkuwa da mutane kudaden fansa har dala milyan 18.34, kwatankwacin naira bilyan 7 kenan.

Rahoton cewa ya yi an biya wadannan makudan kudade a matsayin kudin fansa tsakanin watan Yuni, shekara ta 2011 zuwa Maris, 2020.

Cibiyar SB Morgan ta ce ta yi amfani ne da bayanan kididdiga Cibiyar Bin Diddigin Rikice-rikice da kuma bayanan da jaridu ke wallafawa, ciki kuwa har da PREMIUM TIMES.

Rahoton ya fitar da sunayen wadanda aka yi garkuwa da su, ranar da aka yi garkuwa da su, jihar da aka yi garkuwa da su da kuma adadin makudan kudin da aka biya aka sake shi.

Jihohi 10 da aka fi karbar makudan kudade a hannun mutane domin biyan fansa, duk a yankin Kudu maso Kudu su ke.

Bayelsa 85, Delta 96, Rivers 120, Kaduna 177, Barno 82, Kogi 59, Edo 55, Ondo 54, Katsina 52 sai Taraba 47.

Masu garkuwa sun fi karbar makudan kudade a yankin Kudu maso Kudu, saboda ba haka kawai suke tare hanya su kwashi fasinjoji su nausa jeji ba.

Rahoton ya nuna yadda masu garkuwa ke tsayawa su darje, sai hamshakin dan siyasa, ko wani kasurgumin mai hannu da shuni.

Saboda sun maida abin sana’a, sun fi hamshakai, ko iyalan su, yadda za su karbi milyoyin nairori.

Rahoton ya ce ba su cika kashe wanda suka yi garkuwa da shi ba, sai fa wanda ya ki ko ya kasa biyan diyyar kudin fansa.

A yanzu kuwa, masu garkuwa da mutane, musamman Arewa, ba zu tsayawa zaben wanda za su yi garkuwa da shi. Sabanin kafin 2020, yadda a da sai sun darje.

Kwatsam sai kuma aka wayi gari garkuwa da mutane ya zama wata harkar neman kudi a Arewa, musamman a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto, Kaduna, Neja da sauran su.

Yawancin a nan ‘yan bindiga ne ke yin garkuwa da mutane, tare kuma da kai muggan hare-hare da rugage, kauyuka da garuruwa.

Garkuwa da mutane ya kara kamari a jihohin Kaduna, Rivers, Katsina, Zamfara, Taraba, sai Bayelsa.

Ana ganin cewa rashin aikin yi ne ya kara kazamcewar lamarin. Sannan kuma an yi kintacen cewa a wasu yankunan da aka maida garkuwa hanyar samun makudan kudade, lamarin ya fi karuwa idan zabe ya gabato.

An danganta mafiya da cewa a kara wa jami’an “yan sanda horo, sannan kuma a fito da wani sabon shirin farfado da tattalin arziki a kasar nan.

Share.

game da Author