ƘALUBALEN TAFIYATA DAGA KANO ZUWA ABUJA: Yadda manyan titinan Najeriya suka zama kasuwar hada-hadar naira tsakanin direbobi da jami’ai

0

Ko shakka babu, kowa zai yadda da ni cewa dokar zama wuri ɗaya (lockdown) a sakamakon cutar Kwaronabairus ta tada ƙura tuli wadda ta sa mutane ba sa iya ganin gabansu balle kuma sanin ina suka nufa a sakamakon hakan an samu ƙalubale masu yawa ta fuskar kasuwanci da rashin kewayawar kuɗi a hannun al’umma tare da ma rashin samun albashi ga masu aiki a kanfanoni da masana’antu da makarantun masu zaman kansu.

Sannin kowa ne cewa gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna na sawun gaba-gaba wajen yaƙi da cutar da al’umma kansu har yau ke kokwanton ko ma akwai ta a gaske a garuruwansu ko dai ita ma cutar tana yin abin nan ne na “mutuwa ɗauki ran matsokaninki” saboda tana kama masu ziyare-ziyaren ƙasashen waje kaɗai da muƙarrabansu. Wannan ta sa wucewa ta Kaduna daga Kano zuwa Abuja tamkar tsallaka siraɗi ne mai ƙarfin tsarga zuciyar matafiya da damuwa. Wannan ta sa a yau nake son ba ku labarin irin ƙalubalen da na sha a wannan hanya ta Kano-Kaduna-Abuja tare da bayyana ra’ayina a kan wasu muhimman al’amura kamar haka:

Kamar kodayaushe, bayan sallar Asuba, a kan ɗan sake rintsawa. Hakan kuwa ce ta faru a wannan rana ta Juma’ar 19 ga watan Mayu, 2019. Inda, da misalin ƙarfe 6:30 na hantse baccina tare da miƙewa don yin shirin karyawa. Saidai na fara da saka cajin waya domin na kwana wayata na ƙugin “battery low” kamar cikkunan talakawan Nijeriya saboda yunwa.

Kwatsam! Sai tunanin yin tafiya ta faɗo min kasancewar a baya na yi niyyar tafiya kuma har mota na hau a tasha, amma tun a hanya motar ta lalace, ga kuma batun rufe hanya da aka yi. Wannan ta sa dole muka yo mi’ara-koma-baya. A yau, sai na ce bari na kira ɗan kamashon motocin hayar don jin ko ya yanayin tafiya take tun da Kano a buɗe take? Nan take Muhamman Sani ya tabbatar min da cewa har mota ɗaya ta yi gaba, ma’ana akwai tafiya kenan. Wannan ta sa ni yin gaggawar sanar da mahaifiyata don tahowa. Nan kuwa ta amince kuma na yi futar burgu sai tashar Na’ibawa da ke Kano ba tare da sanar da aminina ba Abdulhadi wanda tare da sauran abokaina kan raka ni hawa adaidaita-sahu.

Da zuwa na tarar da fasinjoji danƙam kamar waɗanda suka taru don karɓar tallafin gwamnati na hatsi ko kuɗi.

Tallafin da minista Sadiya ta Hukumar ba da Agaji tai iƙirarin tana rabawa, amma fa irin rabon nan na namu-namu su tattaho, sannan na nasu-nasu su warwatse domin kuwa kam cikin garin Kano ina tabbatar da ba wanda ya ga ko ƙeyar wanda ya ga wanda ya karɓi wannan tallafi. Kamar dai yadda ba wanda ya san wanda ya san wanda ya san wanda ya kamu da cutar Kwarona kuma aka kwantar da shi a Kano. Na matsa muka gaisa da Muhamman Sani wanda ya nuna min motar da zan hau tare da cewa an yi min ragi na 1000 a maimakon 5,000 da ake biya. Ni ko daɗi ma ban ji ba, domin ko a baya ma da man fetur ke tsada ainun kamar guzurin mayya, ina biyan naira 2,000 ne kuma ko da lokacin Kintsa-Mushe ne, to ba ya wuce 3,000, ba yanzu da man fetur ya karye warwas. Haka nan na biya kuma na shiga mita kamar sauran fasinjoji a kan tsadar kuɗin mota. Shi kuwa direban, wani farin matashi mai hanci, ustazu, domin ko a mota karatun ƙur’ani ya sa mana duk da aljihun baya na da yawa a motar bai gajiya ba wajen ba mu haƙuri da cewa; “ba ku san ya hanyar nan take ba ne.” Mu kuwa, wasunmu na amsawa da, “ba wani nan. Kawai dai don kun ga Kwarona ne.”

Tun a hanya, ƴan karota suka karɓe wata takarda mai ɗauke da sunayenmu wacce ta ke kamar tikitin kulob wacce in ba ita ba shiga, in ba ita ba fita. Tun kafin fita daga Kano direban nan fa ya yar da hanya ya ɗau wata da ta nausa jeji.

Kamar kodayaushe, ina gaban mota, don ban cika girma da tsayi ba, don haka gaban mota daga tsakiya ke kasancewa wajen zamana. Nan na tambaye shi mai ya sa, sai ya ce min, “akwai kotun tafi da gidan ka da kuma jami’an tsaro. Muna zuwa za su tattare mu da maka mana tara ta dubu goma. Nan ma fa kowa yai tsit, aka zuba wa saurautar Allah ido. Shi kuwa ya yi ta bin daji da ƙauyuka da muke ta ratsawa wanɗanda ta kaici ya kamani nake cewa; “ko ina masu neman wa za su taimaka wa? Ga masu neman taimako nan kuma musulmai!

A haka muka ɓulla Zariya kuma muka fara cin karo da ƴan sanda waɗanda ke karɓar a ƙalla daga naira 200 zuwa sama. Kai! Jami’in tsaro na farko ne ya fi ɗaure min kai shi ne na hukumar FRSC wanda ya tubure kan cewa shi ba zai karɓi komai ƙasa da ɗari biyar ba, haka ya karɓi muƙullin motar tare da shan kunu. Nan na jiyo su kamar ƴan kasuwa suna ciniki da direbanmu har aka daidaita a ɗari bakwai.


Haka nan duk inda muka tsaya, dama jawabin shi ne “yi abin arziƙi ka wuce.” Kaina bai gama ɗauruwa tamau ba, sai da muka zo cikin Kaduna, inda muka tarar da KOTUN TA FI DA GIDANKA sun kafa rumfa a bakin hanya ga kuma jami’an tsaro sun cike ko’ina, sai hayaniya da tsawar muryarsu ake ji, sun ma mance da haƙƙin ɗan’adam na kar a tsorata shi haka nan.

Bayan mun isa na ga hankalin direbanmu ya dugunzuma sosai kamar wanda ƴan boko haram suka tare a Damaturu, sai na tambaye shi me ya faru, nan fa ya shaida min cewa, to a mun zo kotu, kuma sai mun biya naira 10,000 ko ma fiye za mu wuce.

Su fa kotun ta fi da gidanka a bisa tsari na aikinsu kamar yadda na ji wani masani ya faɗa shi ne, su kama masu karya doka tare da yi musu tara wanda gwamnati za ta sanar da kuɗin, sannan kuma su tabbata masu ababen hawan sun biya tare da JUYAWA BAYA SU KOMA INDA SUKA FITO, amma ina, a wannan kotu, na ga yadda ake zabga ciniki kamar a kasuwar ƙwari. Domin da farko direbanmu kasancewar sa Bakano ne mai son naira, sai ya fara da ƴan dabaru, inda ya ajiye motarsa tare da takawa har wurin. Da ƙarasawarsa ya dubi wani jami’in tsaro ya karanta masa bayani, shi kuwa da yangarsa ya sanar masa cewa, to fa in yana so ya taimaka masa wajen biyan 5,000 a matsayin kuɗin tara, to fa “ya yi abin arziƙi,” wato sabuwar hanyar karɓar na goro. Nan fa direban ya ciro dubu guda masu dattijai biyu ya sinna musu ita. Da amshewarsa kuwa, sai ya ce, “yanzu ka yi magana!”

Alƙalan dai su uku ne zaune a kan kujerar roba suna ta hada-hada, nan fa suka shiga daka tsawa suna cewa ina motarka? Shi kuma yana amsawa da tana baya saboda “go slow.” Abin ka da masu haɗin baki, sai jami’in nan ya yi masa raɗa kunnensa. Raɗa kuwa tun muna yara muke ji ana cewa, “mai raɗa, mai raɗa ɗan wuta, mai ji, mai ji kafiri.” Amma haka nan suka yi suka gama. Da ƙyar da tsawa, wai su ga masu gaskiya, suka yadda suka karɓi naira 5,000 tare da ce masa ya je. Amma Bakano da wayo, sai ya ce, “yallaɓai ina rasiti?” Sai fa yallaɓai ya ɓata fuska ya rubuta ya miƙa masa. A jiki na ga an sa naira 10,000, amma fa mu 5,000 muka biya. Da dawowa wurin mota, sai ya ce kowa ya shiga, nan muka wuce, babu wanda ya ma tuna da wata “social distancing,” domin a motar huɗu-huɗu-uku aka yi irin na ƴan ƙwallo.
Abin takaici kuma shi ne, na ɗauka batun cin hanci ya ƙare, amma sai na ga duk inda muka tsaya sai su ce mana ina rasiti? Direbanmu kuma ya nuna, sai ka ga sun yi wata bazaurar dariya sun ce “yauwa, wannan na laifin shigowa ne, sauran kuma alherinmu!” Kuma su fa ba sa karɓar naira 100 sai fa manyan kuɗi kamar 500 zuwa sama. Nan na ji tausayin direba ya kama ni. Duk da na san ya karya doka na ɗaukar mu ya biyo hanya saboda dokar kulle, to amma su kuma jami’ai da kotunan can su kuma mene ne HUKUNCINSU? Abin ɗaure kai kuma wasu jami’an, ko takunkumi ba sa sawa, balle wani tazara. Wasu direbobin dai kan dakata ne daga nesa, har zuwa biyar na yamma bayan kotunan kan hanya sun ci kasuwarsu sun tashi, sannan sai su zo su wuce salin-alin, sai fa sauran jami’an tsaro waɗanda da ka ba su “abin arziƙi” to ko bindigogi ne direba ya ɗebo zuwa Katsina ko ma Sakkwato inda ake ta KASHE al’umma, to fa ya sha kenan, in ji yara masu wasan langa. Kuma ko da a daren ranar Alhamis a kano, haka ƴan sanda suka tare mu a mashin mai-ƙafa-uku bayan mun dawo da misalin ƙarfe 10:00 na dare daga duba ɗan uwanmu da ya karye kuma babu wani bincike, sai suka ce mana mu yi abin arziƙi kawai mu wuce. Ba sa son mu ɓata musu lokaci. Ya Ilahi, ta haka za a samu CIKAKKEN TSARO A ƘASA BAYAN JAMI’AN ABIN DA YA DAME SU SHI NE NA GORO KAWAI.

Ni dai da haka na iso Suleja, na gode wa Allah. Tun da dai Kanon ma kasuwancin ya tsaya ga ƴan kuɗaɗena na albashi sun tasamma ƙarewa saboda zaman ƙulle na dole. Wai a haka, ma ni da sauƙi sosai.

Domin ma’aikatan da gwamnati ta zabtare wa albashi na san yanzu sun ɗan cinye abin da ya shigo musu na watan; maimakon su ga tallafi, sai ma su ke ba wa gwamnatin tallafi. Wannan ne fa mara ƙarfi ya ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi duk da kuwa uban basussuka da gwamnatin tarayya ke jidowa kamar mai shirin sayar da ƙasar nan.

Tambayoyin su ne:

Wani yunƙuri Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka (NCDC) ke yi wajen gamsar da al’umma da bayanai na gani ya kori ji ga kan wannan cuta domin har yanzu jama’ar garuruwan Nijeriya ba su amince da alƙaluman da suke wallafawa ba a shafukansu na sada-zumunta?

Wane Yunƙuri gwamnatin Tarayya mai iƙirarin yaƙi da cin hanci ke yi da gwamnatocin jihohi da kuma Hukumar Rundunar Ƴan sanda wajen magance karɓar na goro da jami’an tsaro ke yi a hanyoyi daban-daban? Shin ba sa karɓar wadataccen albashi ne ko kuma dai tsabar kunnen ƙashin ne na saɓawa ƙa’idojin hukumomin tsaron?

Dama biyan tara Idan matafiya suka karya doka har aka gurfanar da su a gaban kotun tafi da gidanka wani lasisi ne na cigaba da tafiya zuwa inda za su ko kuma dai so ake su juya da baya su koma inda suka fito? Ya kamata irin waɗannan kotunan su yi wa al’umma bayani in har da gaske ne gwamnoni na ƙoƙarin magance matsalar wannan annoba kamar yadda gwamna Nasir El-Rufa’i ke iƙirari.

Shin yaya kuwa kuke kallon gudunmawar dokar zaman gida dole wajen magance matsalar yaɗuwar wannan annoba ta Kwaronabairus?

Ya batun gaskiyar cewa Hukumar EFCC za ta fara binciken ministar Hukumar ba da Tallafi mai raba tallafin rage raɗaɗi kan zaman gida dole a sakamakon wannan annoba? Ya batun ciyar da yara ƴan makaranta abinci kamar yadda ta alƙarwanta? An fara ko kuwa da sauran rina a kaba, don ni dai ban ga yaran unguwanninmu na ci irin waccen ta-tsotse ba?

Daga, Anas Ɗansalma. Jihar Kanon Nijeriya.

Share.

game da Author