Rayuwar gidan talaka ta dogara ne akan bugabuga da yake yi kullum idan gari ya waye. Wannan rayuwa itace wacce tsuntsu yake yi. Ma’ana, kullum sai ya fita yake iya samun abunda zai ci. Shiyasa duk wanda ya fito daga gidan talakawa ya saba da yunwa saboda idan yau an samu abinci, ba lallai bane a samu gobe.
Allah cikin jarrabawar da yake yiwa bayinsa, sai ya jarrabemu da annobar cutar COVID-19, wacce ta janyo mana zaman gida don a daqile yaduwar cutar a tsakaninmu. Duk da cewa muna fama da talauci da karancin abinci a gidajenmu. Gaskiya a wannan lokacin ne magidanci zai gane ingancin matarsa ta fannin tattalin arziki da rufin ashirin gida.

Tabbas, a wannan lokacin ba’a maganar jin dadi, zaben abinci ko almubazzarancinsa. Idan matarka ta rufin assiri ce, baka da damuwa sosai saboda duk hanyar da zata bi tayi muku dibara a samu abunda za a ci ta sani. Misali, da gari na masara kawai zata iya yi muku abinci kala bakwai: (Tuwo, shashshaka, dambu, danmalele, fatefate, burabusko da dambu)
Idan Allah ya jarrabeki da miji mai karamin karfi dole ki taimaka masa, saboda da wanne zai ji? Talauci ko matsalar matarsa? Musamman a lokacin nan na lockdown. Ya zama dole ki rage awon abincin da kuke ci a baya don ku iya rayuwa a wannan lokacin, ba tare da assirinku ya tonu ba. Idan rabin kwanon shinkafa kuke ci a rana, sai ki mayar dashi gwangwani shida. Hakan zai yiwu kuma har ya isheku, ciki babu ruwansa, abunda baya so kawai a hanashi abinci.
Babban kuskure ne mace ta dinga kushe abinci, wata ma har ‘ya’yanta take koyawa zabe-zaben abinci saboda rashin kan-gado. To gaskiya a wannan lokacin, idan ma fa kuna da abincin kenan, babu maganar zabe-zabe, babu maganar neman dadi saidai neman a fita hakkin ciki ta ko wani hali.
Ki gwada ki gani, idan har kina da wannan nagartar da na lissafo a baya, to sunanki matar rufin assiri. Idan kuma babu, to zaman hakuri ake da ke.
Ana iya gane ingancin mace a lokacin da ake cikin wahalar rayuwa. Ba a cika gane nagartar abokin zama ba idan ana cikin arziki. Talauci ne yake tona assirin mace, kamar yadda arziki yake tona assirin miji. Namiji idan yana da kudi an fi gane cikakken halinsa, ita kuma mace tafi nuna mugun hali idan aka shiga talauci.
Tabbas, magidanta da yawa suna fargabar wannan doka ta “lockdown” ne saboda rashin wadata da kwanciyar hankali ta matansu. Gaskiya yakamata matan gida ku daure ku ci jarabawar wannan lokacin. Ki yiwa yaranku tarbiyar yin hakuri da rayuwa. Hakuri yana maganin komai a rayuwa.
Allah ya karemu.