Za a fara bi gida-gida ana yi wa mutane gwajin coronavirus a Abuja

0

Mahukunta a Babban birnin tarayya, Abuja sun bayyana cewa ma’aikatan lafiya za su fara bi gida-gida domin yi wa mutane gwajin coronavirus.

Mahukunta a Abuja sun ce za a yi haka ne domin dakile yaduwar cutar.

Shugaban kiwon lafiya ta Abuja Josephine Okechukwu ta Sanar da haka a wata takarda da aka aika wa PREMIUMTIMES.

Josephine ta ce ma’aikatan kiwon lafiya za su bi unguwanni domin yi wa mutanen dake nuna alamun kamuwa da cutar kamr yawan yin tari, ciwon kirji, zazzabi, yankewar mumfashi da sauran su.

“Mun fara gwajin ranar Litini a yankin Mpapeza zamu shiga unguwannin Gishiri, Utako da Mabushi as tsakanin Laraba da Alhamis.

Shugaban kwamitin dakile yaduwar coronavirus a Abuja Aliyu Umar ya ce akwai yiwuwar za a samu karin mutanen dake dauke da cutar a Abuja a dalilin yin wannan gwajin.

“A yanzu dai Abuja ta yi kwanakin uku rabon da a samu mutanen da suka kamu da cutar amma a dalilin yin wannan gwaji,za a iya samun mutanen da suka kamu da cutar.

Umar ya yi kira ga mutane da su ba ma’aikata hadin kai.

Akalla mutane 362 ne suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya. Abuja na da mutane sama da 50 da suka kamu. Jihar Legas ce tafi yawan wadanda suka kamu da cutar.

Mutane samam da 100 sun warke a najeriya har an sallame su.

Share.

game da Author