Da farko dai ina so na taya al’ummar jihata ta Kano alhinin barkewar cutar COVID-19 a jihar Kano. Tun kafin mu fara tabbatar da samuwar mai cutar COVID-19 na farko a Kano, a lokacin bamu da cibiyar gwajin cutar a jiharmu, wani kwararre a kan harkar annobobi da ke zaune a kasar Amurka, ya yi hasashe a kan abubuwan da ya kamata mu lura da su dan gane cewa ko cutar ta riga ta bulla jihar Kano ba mu sani ba. A cikin abubuwan da ya lissafa akwai maganar cewa idan mun ga ana yawan mace-mace, musamman na tsofaffi da kuma yawan masu ciwon zazzabi da mura, toh mu fara zargin cewa cutar ta riga ta fantsama a cikin al’ummar mu.
A kwanakin bayan nan mutane da yawa sun koka a kan yawan mace-mace musamman na tsofaffi a Kano. Kullum na zo shafi na na facebook sai na ga mutane da yawa sun saka sakon ta’aziyya a shafukansu. Haka kuma mutane da dama a unguwanni daban-daban suna ganin kamar adadin mutanen da ake binnewa a makabartunsu ya karu sosai.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba shine tana iya yiwuwa ba karin mace-mace aka samu ba, yawan zaman gida da mutane suke yi a wannan lokacin ne ya sa adadin mutanen da suke da lokacin yin rubutu a kafafen zamani na sada zumunta ya karu, saboda haka adadin masu rubuta sakon ta’aziyya ya karu, mu kuma muke ganin kamar adadin mace-mace ne ya karu. Tana kuma iya yiwuwa yawan mace-macen ya karu amma ba saboda cutar COVID-19 ba. Wata kila sakamakon rufe gari da aka yi ne ya sanya marasa lafiya ba sa iya ganin likita da wuri har sai ciwonsu ya ta’azzara sun mutu a gida.
Ko ma wane dalili ne ya jawo wannan al’amari, abu ne mai matukar muhimmanci a ce gwamnati ta bincika lamarin. Yin hakan zai bata dama ta san halin da ake ciki dan ta kara zage damtse ko ta san wasu irin karin matakai zata dauka dan dakile wannan cuta.
Akwai hanyoyi da dama da gwamnati za ta iya bi dan samun karin haske a kan wannan al’amarin. Zan kuma jero su kamar haka:
1. Gwamnati za ta iya tattara bayanai daga dukkanin masu kula da makabartun kano domin ta ji ra’ayinsu akan cewa ko suna ganin adadin mutanen da ake binnewa a makabartun da suke kula da su ya karu. Wannan zai baiwa gwamnati haske wurin ganowa ko adadin mace-mace ya karu. Za ma a iya hadawa da tambayar su shekarun wadanda suka mutu a kwanan nan dan samun karin haske. Misali, yan shekaru nawa aka binnewa?
2. Gwamnati za ta iya fara karbar bayanai akan adadin mutanen da aka binne a kowace makabarta a a kowace rana a Kano daga yau dinnan ko gobe. Idan aka ga adadin yana karuwa kullum to alama ce da ka iya nuna cewa adadin mace-mace na karuwa.
3. Gwamnati za ta iya yin kwarya-kwaryar bincike ta tambayi iyalan wadanda suka mutu a Kano a kwanakin nan dalilan mutuwarsu. Ma’ana wace iriyar rashin lafiya suka yi kafin su rasu. Menene da menene ya ke damunsu kafin su rasu? Ciwon kai ne? Zazzab nei? Ko menene? Wannan zai baiwa gwamnati haske a kan irin cututtukan da suka kashe mutane a kwana-kwanan nan.
4. Gwamnati za ta iya sanya dokar duk wanda za’a binne a kowace makabarta a jihar Kano sai jami’anta sun gwada gawar dan ganin ko tana dauke da cutar COVID-19. Sai ya kasance ta girke ma’aikatanta a dukkan makabartu da unguwanni dan a rika kiransu suna daukan abin gwaji a jikin gawar kafin a hada ta. Duk da cewa wannan abu ne mai matukar wahalar yi. Duba da yanayin zafin mutuwa da ke tattare da wadanda suka rasa nasu, wannan shawara ce da ya kamata a jinkirta ta ko kuma a yi mata kwaslwarima.
5. Gwamnati za ta iya yin kwarya-kwaryar bincike ta dauko bayanai daga asibitoci dan ta duba wasu matsaloli ne suke addabar mutane suna kawo su asibiti kafin bullar wannan cuta da bayan bullarta. Wannan zai bai wa gwamnati haske wurin ganowa ko cutar COVID-19 ta riga ta fantsama a jihar Kano.
A karshe dai yana da matukar muhimmanci a ce gwamnati ta binciki wannan matsalar ta yawan mace-mace musamman a wannan lokacin da muke ciki na zullumi. Ya kuma kamata gwamnati ta yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran kungiyoyi su tallafa mata a wannan gagarumin yakin.
Allah ya fitar da mu da cikin wannan kangin da muke ciki.
Ameen.
Dr. Abdulaziz Tijjani Bako, MBBS, MPH, PhD (cand). Likita ne mai bincike a kan harkar lafiyar al’umma a Jami’ar Indiana University da ke kasar Amurka