‘Yan siyasan jam’iyya mai mulki na sace kayan agaji a Kaduna – Kungiya

0

Cibiyar Cigabar Dimokradiyya (CDD), ta yi korafin cewa ”yan siyasan jam’iyya mai mulki wato jami’an gwamnatin APC a Kaduna, na yin babakere da kuma sace abincin tallafi da aka ware wa talakawan jihar.

Darektan CDD, Idayat Hassan ta shaida cewa wadanda yaka mata su samu wannan tallafi ba sune suke samu.

A karamar hukumar Kaduna Ta Arewa maimakon a rabawa talakawa, da an kawo kayan tallafin sai ‘yan siyasa masu mulki su yi babakere su rufe ko’ina sannan su aika da su gidajen su. Hakan ya sa talakawa da yawa basu samun wannan tallafi na gwamnati.

A unguwanni kamar su Narayi, Kudenda da Doka, duk irin haka ‘Yan siyasa suka rika yi. ” Akwai inda aka kawo katan din Indomie 300, da galan-galan na man gyada har 109 amma maimakon a ba talakawa da gajiyayyu sai kawai ‘yan siyasa suka yi awon gaba da su suka rabawa wa kansu.

CDD ta gano cewa babu wani tsari da akayi na yadda za a yi rabon kayan abinci na tallafi a jihar Kaduna sannan kuma ba a samar da yanayi da zai kare mutane daha cakuda wuri daya ba don kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus.

Akan cunkusu ne wuri daya kawai ayi ta kokawar karbar abinci.

Cibiyar CDD ta ba gwamnati shawara da ta canja salon yadda ake rabon kayan abincin.

Sannan kuma lallai a binciki yadda aka raba na baya, kuma kamata yayi a shirya jadawai ta musamman da zai kunshi sunayen mutane a unguwannin jihar domin a raba musu tallafin.

Share.

game da Author