Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya Sanar da saka dokar zaman Gida dole na kwana bakwai a fadin jihar.
Hadimin gwamna Ganduje kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Yakasai, ya sanar da hakan a takarda da ya raba wa manema labarai a Kano.
Yakasai ya ce gwamna ya saka wannan doka ce a dalilin sake bankado wani a jihar da ya kamu da Coronavirus.
” Wannan doka ta zama dole a saka ta domin a dakile yaduwar coronavirus a jihar. Sannan kowa dole ya bi wannan doka ko kuma ya kuka da kan sa.
Jihar Kano ta shigar sawun Jihohin kasar nan da suka kamu da cutar coronavirus a makon da ya gabata.
Tun daga wannan rana ake ta samun karuwar wadanda suka kamu da cutar.
A Najeriya akwai mutum 343 da suka kamu cutar.