Wani likita a asibitin da aka fara duba mutumin da ya fara kamuwa da cutar Coronavirus a Kano, ya shaida wa PREMIUM TIMES yadda mamacin, wanda ya rasu ranar Laraba ya boye musu bayanan ainihin abin da ke damun sa, kafin a kwantar da shi a ranar 10 Ga Afrilu.
“Kafin a kai ga kwantar da shi, ya zo ya ce mana ya na fama da zazzabi, bushewar makoshi, kuma ba ya sha’awar cin abinci. Mun tambaye shi ko ya na fama da tari, sheshsheka kuma ko ya ziyarci wata kasa kwanan nan, sai ya ce a’a.” Inji Likita James King.
“Sai daga baya mu ka gano cewa mamacin ashe ya yi balaguro zuwa kasashen waje. Ya dawo ta Abuja. Daga can ne ya karaso nan Kano a mota.” Haka likita James na rubuta a shafin sa ba Facebook, inda ya kara da cewa mamacin ya yi mu’amala da ogan su, sai shi James din da kuma wasu jami’an lafiya uku, sai ma’aikacin su daya, wanda ba likita ko jami’an kula da lafiya ba.
Da ya ke zantawa da PREMIUM TIMES a yau Alhamis, likitan ya ce ya baza wannan bayani na sa a soshiyal midiya, domin likitoci da jami’an kula da lafiya su rika kaffa-kaffa.
“Mutumin nan duk ya ki fada mana gaskiya, amma mun gano kafin ya karaso Kano daga Abuja, ranar 25 Ga Maris, har Kaduna ma ya yada zango.”
“Sannan kuma duk bai fada mana cewa can a Abuja an ma debi burtsatsin sinadaran jikin sa a Cibiyar NCDC, domin a yi masa gwaji ba.
King ya ci gaba da cewa ba su sani ba, ashe mutumin, wanda tsohon jakada ne, ya je wasu asibitoci ba daya ba, kafin ya zo Kano.
“Da ya zo Kano kuma ya je Sallar Juma’a, kuma ya halarci tarukan daurin aure.
“Bayan an kwantar da shi asibitin mu, a ranar Asabar din sai wani abu kamar wasan kwaikwayo ya faru, inda ‘yan sanda suka mamaye titin d ke nufa asibitin mu, ba shiga, kuma babu fita.
“Mun yi sa’a a lokacin babban likitan mu ya na nan, ya na tiyatar kwakwalwa, aka shaida masa cewa jami’ai sun ce akwai mai cutar Coronavirus a asibitin mu.
“Nan da nan, ya fito, suka ce masa, ” akwai umarni daga Gwamna cewa akwai mai dauke da cutar Coronavirus a nan, saboda haka an ce mu gaggauta kulle asibitin, don kada saura su kamu.”
James ya ce shi da sauran ma’aikatan duk sun killace kan su, an kuma dauki sinadaran jikin su, an yi musu gwaji. A ranar 15 Ga Afrilu sakamako ya fito, an ce ba su kamu ba.
Wata kungiya mai suna Kungiyar Matasan Kano, ta nemi Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya kafa bincike, domin a gano gaskiyar zargin da ake yi cewa da gangan mutumin ya shigo Kano dauke da cutar, domin ya baza ta a cikin jama’a.
da yawa daga cikin mutanen Kano da na Najeriya ma sun nuna bakin cikin su kan abinda wannan mutum yayi. Wasu na ganin ya ci amanar mutanen Kano da na Najeriya. Domin ya rika zsazzagayawa yana halartar Salloli, Bukukkuwa, taron suna da sauran su duk da ya san baya jin dadi.
Haka kuma da gangar ya ki fadi wa mutane gaskiyar abinda yake tare da shi. Hatta gwajin da NCDC suka yi masa bai sanar da mutane ba, da likitoci.