Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya, Mal Uba Sani yayi na maza inda ya yunkuro don share wa miliyoyin talakawan gundumar sa hawaye.
Sanata Uba Sani na wakiltar gundumar Kaduna ta Tsakiya ne a mjalisar dattawa da suka hada da Kaduna Ta Arewa, Kaduna Ta Kudu, Kajuru, Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun.
Sanata Uba ya samar da dubban buhunan abinci dabam-dabam da za a raba wa gidaje akalla miliyan biyu dake karkashin gundumar mazabar da yake wakilta a majalisar Dattawa.

Da yake kaddamar da sauke tireloli akalla 10 na abinci kala-kala, wakilin Sanata Uba Sani, Rabiu Abubakar ya ce ba anan sanatan zai tsaya ba. Zai ci gaba da share wa talakawa hawaye har sai inda karfin sa ya kare.
Ya kara da cewa makasudin yin haka shine don taimakawa mutane musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin rayuwa a dalilin annobar COVID-19 da kuma azumin watan ramadan da aka shiga.
Wadannan kayan abinci da za a raba sun hada da buhunan shinkafa, gero, da siga. Sannan kuma za a raba wa kungiyoyin addinai, kungiyoyin mata, gidajen marayu da marasa galihu ne.
Jama’an gari da mutanen kananan hukumomin da ke karkashin gundumar Sanata Uba Sani sun yaba matuka sannan sun jinjina wa sanatan bisa tausayi da yake dashi da kokarin sa na share wa talaka hawaye.
” Mu mun san cewa ba mu zabi tumun dare ba domin kuwa, sanata Uba Sani tun kafin ya tafi majalisa ya ke abin azo a yaba. Muna godiya Allah ya karo irinsu.” Insa Sani Jibrin, mazaunin Kaduna.