” Ba gaskiya ba ne da Shugabannin Majalisa suka ce shirin Bayar da Tallafi (NSIP) ya karbi ya lamushe naira tiriliyan 2 daga 2016 zuwa yanzu.
“Da farko Majalisar Tarayya ta amince a cikin kasafin kudi a ba raba naira tiriliyan 1.7. Amma daga 2016 zuwa Oktoba, 2020 lokacin da aka maida komai a karkashin Ma’aikatar Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, naira bilyan 619.1 kadai aka ba mu. Wato kashi 36% bisa 100% kadai na kudaden.”
Maryam ta kuma karyata ikirarin da shugabannin majalisa suka yi cewa ta tsarin BVN suke raba kudade.
Ta ce kudaden rage kuncin talauci da ake tura wa mabukata a asusun ajiyar banki, daga Ma’aikatar Tsare-tsare ta Jihohi suka samu alkaluman wadanda ake bai wa kudaden, ba ta tsarin BVN ba.
Ta ce tsari ne da ake bi tun daga kananan hukumomi ana tantance wadanda suka cancanta su amfana.
Ta ce sai an tantance a ina gida ya ke? Mutum nawa ne a ciki? Maza nawa ne kuma mata nawa ne?
Maryam ta ce karya Shugabannin Majalisa ke yi da suka ce majalisa ta kasa gane tsari, matakai da ainihin ilahiri da adadin wadanda ke amfana da kudaden a gaskiyance.
Ta kara da cewa ana aika wa majalisa da kwafe-kwafen bayanan da ke tattare da duk bayanan da ake bukata na rabon kudaden.
“Da suka ce tsarin biyan kudaden tallafi ta rajistar NSR damfara ce, wannan abin takaici ne matuka, kuma ganganci ne, kasassaba ce kuma wauta ce.”
Maryam ta ce wannan shakku da tababa da Majalisa ta nuna zai iya zama barazana ga sake karbar kudaden da iyalan Abacha suka kimshe. Saboda shirin NSIP yarjejeniya ce da Bankin Duniya, masu sa ido a kan kudaden.
A karshe ta ce tun cikin Sarumba 2019 aka maida shirin a Karkashin Ma’aikatar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwa. Amma ta zabi ta maida martanin ne domin
da tukura da bako, duk Umbutawa ne, kuma abin da ya ci garin Doma, ba zai bar garin Awai ba.