Yadda matasa ‘yan sababi da hasalallun masallata suka yi wa Jami’an Yaki da Coronavirus rajamu a Masallacin Agege

0

Jami’an Kwamitin Yaki da Cutar Coronavirus da kuma Tilasta Zaman Dirshan a Gida na Jihar Lagos, sun sha ruwan duwatsu daga wasu hasalallun masu sallar jam’i a Babban Masallacin Agege da ke Lagos.

Babbar Manajar Hukumar Tsaftace Muhalli (LASEPA), wadda kuma ita ce shugabar jagorar Kwamitin Tilasta wa Jama’a bin Doka, Dolapo Fasawe, ta ce su na isa babban Masallacin Agege, sai suka iske daruruwan masallata na jam’in Sallar Magriba.

“Akalla za su kai su 300, domin akwai jama’a dankam a masallacin. Mu na isa sai wasu matasan unguwa ‘yan sababi su ka rufe motocin mu da jifa, suka yi ma na kofar-raggo.

“Su kuma masu sallar jam’i, su na sallamewa sai su ka darkake mu da jifa, su da matasan su ka rika antaya ruwan duwatsu

“Tun da farko mun yi kokarin ganawa da limamin, Amma abin ya faskara, saboda wurin ya hautsine da yahaniya da rudani.

“Mun yi mamakin ganin yadda su ka kai mana hari, domin kafin ma a kafa dokar sai da muka rika bin wuraren ibadu, ciki har da Babban Masallacin Agege muna wayar musu da kai, cewa ba ibada aka hana ba, amma abin da dokar Jihar Lagos ta ce, idan aka gwamutsu wuri daya, to wani zai iya kwasar cutar daga cikin gungun jama’a ya kai ta cikin iyalan sa, daga nan su ma su kwasa wani ya kamu daga gare su.

Idan za a tuna dai Jihar Lagos ta kafa dokar zaman gida kuma hana walwala. Ciki kuwa har da taron yin ibadar Kiristoci da sallar jam’i.

Ta ce wata barazana ba za ta hana su gudanar da aikin su na ceton rayuwar jama’a ba. Kuma ta Yi kira ga mutane a kara kiyayewa.

Shi ma Shugaban LASEPA na Jihar Lagos, Lanre Mojola, ya ce ba za su nuna sarewar guyawu daga aikin da ke kan su ba.

Share.

game da Author