Kwamitin dakile yaduwar cutar Covid-19 dake jihar Barno ya Sanar cewa mutum 4 ne ke dauka cutar a jihar.
Shugaban kwamitin kuma mataimakin gwamnan jihar Umar Kadafur ya Sanar da haka wa namema labarai ranar Talata a zama da kwamitin ya yi.
Kadafur ya ce ma’aikatan kiwon lafiya sun fara nemo mutanen da suka yi cudanya da shi.
“An dauki jinin mutum 48 inda sakamakon gwajin ya nuna cewa 44 basu kamu da cutar ba.
“Ana jiran sakamakon gwajin mutum 4 wanda hukumar NCDC za ta aiko nan ba da dadewa ba.
Idan ba a manta ba a ranar Litini ne NCDC ta fitar da sakamakon gwajin da ta yi ranar Litini inda sakamakon ya nuna cewa mutane biyu na dauke da cutar sannan daya ya mutu a jihar Barno.
YADDA JIHAR TA SAMU KARIN MUTUM DAYA
Kadafur ya ce wani matafiyi daga Legas ya shigo da cutar jihar Barno.
Ya ce matafiyin ya yada zango a jihar Gombe inda a nan ne aka gano ya kamu da cutar.
Kadafur ya ce Wannan matafiyi na cikin mutum biyar da suka kamu da cutar a jihar Gombe.
Ya ce daga nan ne gwamnatin jihar Gombe ta aiko da mutumin jihar Barno inda aka kwantar da shi a asibitin Biu sannan daga baya aka maida shi asibitin kula da masu fama da cutar a Maiduguri.
A yanzu dai mutane 4 ne ke dauke da cutar daya ya mutu a jihar Barno.