Yadda mai dauke da coronavirus ya nemi arcewa daga wurin da aka killace shi a Kaduna

0

Wani dake dauke da cutar coronavirus a wurin da aka kebe don killace masu fama da cutar a Kaduna, ya nemi ya arce da karfin tsiya daga inda yake a killace.

Wannan mutum ya dauke mukullan kofar shiga wajen killace masu fama da cutar a Kaduna. Daga nan sai daya daga cikin jami’an da ke kula da wannan wuri ya taro shi a guje ya cafke shi ya maida shi daki.

Kakakin wannan cibiyar, Ekunola Gbenga ya shaida cewa jami’in da ya kamo wannan mutum Joshua Philip, ya fada cikin hadarin kamuwa da wannan cuta.

” Yanzu dai mun ba jami’in damar ya je gida ya killace kansa na kwana 14 domin sanin yadda abubuwa za su kasance. Idan yaji ba dadi ya garzayo maza-maza a duba shi.

Shi wannan mutum da ya nemi arcewa daga wurin killace marasa lafiya ne wai shi yana so ya tafi yin addu’a da sanyin safiyan, su kuma jami’ai suka hana shi. Daga nan ne yayi sanda ya dauke mukullin kofar gidan ya nemi fita da karfin tsiya.

Haka kuma a jihar Osun a kwanakin baya wasu mutane shida suka arce da ga wurin da aka killace su. Da kyar gwamnati ta kamo biyar cikin su.

Share.

game da Author