Yadda gobara ta lashe matsugunai 700 na ‘yan gudun hijira a Barno

0

Akalla bukkokin masu gudun hijira 700 ne gobara ta lashe kurmus, a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Karamar Hukumar Mafa, cikin Jihar Barno.

Sakataren Karamar Hukumar Mafa, Mohammed Lawan Sheriff ne ya tabbatar da haka a lokacin da ya ke hira da manema labarai a Maiduguri ranar Talata.

Ya ce dimbin jama’a sun rasa matsugunan su sanadiyyar tashin gobarar, wadda ta barke wajen karfe 11 na safiyar Talata, kuma dauki tsawon lokaci na ta cin wuta.

Ya ce wutar wadda ta samo asali daga cikin wani tanti, ta kama sauran tantinan ne saboda babu gudummawar kashe gobara da gaggawa a sansanin.

Sai dai kuma ya ce masu gudun hijira da ke zaune a sansanin, jami’an CJTF da sauran jami’an tsaro sun yi kokari suka kashe wutar.

“Yayin da mu ka samu labarin tashin gobarar, sai mu ka gaggauta tattaro mazauna yankin aka garzata suka taimaka wajen kashe ta, tun kafin ta kara yin barna fiye da wadda ta yi.”

Sansanin masu gudun hijira a Mafa na dauke da mutum 4,782, wadanda akasarin su duk mata ne da kananan yara da kuma dattawa.

Sheriff ya ce Karamar Hujuma ta sa a yi kidayar dalla-dalla domin a tabbatar babu wani mai gudun hijira da ya salwanta.

Ya ce manajoji 11 masu kula da sansanin aka dora wa wannan aiki. An kuma ajiye motar daukar majiyyaci, ko da daga baya za a samu wanda ya ji rauni.

Amma dai a cewar sa, ba a samu asarar wani rai ba ko daya.

Share.

game da Author