Yadda Fatima ta kashe mijinta saboda tsananin kishi da mahaifiyar sa a jihar Neja

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta damke wata bazawara mai sun Fatima Sani mai shekaru 37 da ta samu da laifin kashe mahaifiyar tsohon mijinta da wuka.

Kwamishinan ‘yan sanda Adamu Usman ya Sanar da haka ranar Litini da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Minna.

Ya ce Fatima na zama a kauyen Gobirawa dake karamar hukumar Mashegu kuma ta aikata wannan mummunar abu ne a kauyen mahaifiyar tsohon mijinta dake Tozon Daji.

Usman ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa a ranar 23 ga watan Afrilu mijinta mai suna Sani Umaru ya saki matarsa Fatima saboda matsalar da su ka samu a auren su.

Da haka ya faru sai Fatima ta je gidan mahaifiyar tsohon mijinta Aishatu Umaru mai shekaru 70 a Tozon Daji ta caka wa mata a tsakiyar zuciya, nan take ko ta ce ga garin ku nan.

Fatima ta ce ta yi haka ne saboda mahaifiyar mijinta ne dalilin rabuwar su da danta.

Usman ya ce tuni an kama Fatima sannan bayan sun kammala bincike za a mika ga kotu domin yanke mata hukunci.

Bayan haka Usman ya ce a ranar 25 ga watan Afrilu rundunar ta fatattakan wasu masu garkuwa da mutane bakwai a kauyen Tufa dake karamar hukumar Gurara.

Usman ya ce wadannan masu garkuwa da mutane sun dade suna addabar mutanen wannan kauye.

Ya ce sai da ‘yan sanda suka yi arangama da masu garkuwan kuma sun kashe mutum uku cikin su.

Share.

game da Author