Yadda dan Jihar Jigawa na farko ya kamu da Coronavirus – Gwamna Badaru

0

Gwamna Badaru Abubakar na Jigawa ya yi karin hasken yadda dan jihar na farko ya kamu da cutar Coronavirus.

A ranar Lahadi ne Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC), ta bayyana mutum 87 su ka kamu da cutar a Najeriya, ciki har da mutum daya na farko daga Jigawa.

Tun kafin nan PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda jihar Kano ta mazaya wa Jihar Jigawa wani dan jihar da aka zarga dauke da cutar Coronavirus, bayan an killace majiyyacin da farko a Kano.

A ranar Lahadi ce Badaru ya bayyana wa manema labarai cewa jihar ta samu mai cutar Coronavirus a karon farko.

Badaru ya ce mutumin mazauni garin Kazaure ne, kuma ya na da kantin sayar da suturun zamani (boutique) a Kazaure.

“Ya kamu da cutar ne a yayin tafiye-tafiyen da ya yi kwanan nan zuwa Kudancin kasar nan.

Badaru ya ce jami’an lafiya na ci gaba da tuntubar jami’an lafiyar garuruwan da ya je domin a yi kokarin zakulo dukkan wadanda aka san sun cakudu d shi.

“An Debi sinadaran jikin sa, an kai an gwada, an kuma samu ya na dauke da cutar. Yanzu haka an killace shi a wurin da ake killace masu dauke da cutar, a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.”

Tuni dai Badaru ya bada umarnin hana zirga-zirga a Kazaure, garin da ke kusa da Daura ta Jihar Katsina, garin da shi ma aka bada umarnin kulle shi cikin makon da ya gabata.

Share.

game da Author