Yadda Boko Haram su ka kashe matafiya bakwai kusa da garin mu – Mazauna Auno

0

Wasu mazauna auno, kilomita 20 kafin Maiduguri, babban birnin jihar Barno, sun bayyana wa PREMIUM TIMES yadda Boko Haram suka yi wa matafiya kwanton bauna kusa da Auno, inda suka kashe matadiya bakwai tare da banka wa mota mai dauke da buhunan wake wuta.

Bayan bugs labarin, wanda da farko Kakakin Yada Labarai na Rundunar Sojojin Najeriya, Sagir Musa ya karyata, to kuma wasu mazauna Auno, kusa da inda abin ya faru, sun shaida wa wakilin mu abin da idon su ya gane musu.

“An kai wannan har wajen karfe 8 na safe, saboda apjoji su dage dokar hana wucewa har zuwa karfe 10 na dare.

“Motar farko bude mata wuta aka yi, saboda an tsayar da shi, amma ya ki tsayawa. An harbe mutum biyu nan take, kamar yadda mu ka ji kara, sannan aka ja fasinjojin cikin motar su 13 aka yi gaba da su.

“Su na cikin tafiya ne a surkukin jeji motar ta lalace. Sai suka bude wa mutanen da ke ciki wuta.”

Haka Malam Bunu mazaunin Auno ya tabbatar.

Shi ma Modu Gana da ke cikin Auno, ya shaida wa PREMIUM TIMES mazauna Auno sun bi sawun maharan a cikin wani burtali, inda suka tsinci gawarwakin mutum shi da. Akwai na bakwai wanda ba matafiyi ba ne, dan garin Auno ne, mai suna Musa.

Ranar Lahadin nan da dare Boko Haram suka yi wa matafiya kwanton-bauna suka bindige mutum bakwai, kuma suka banka wa tirela mai dauke da buhunan wake wuta.

Lamarin ya faru kusa da garin Auno, da ke kilomita 20 kusa da Maiduguri, a kan hangar Damaturu.

Wanda ya gani da idon sa ya tabbatar da cewa sun iso kusa da kauyen auno, “sai mu ka ci karo da gawarwakin mutane a kan titi.

“Sannan kuma na ga motoci biyu da aka banka wa wuta. Daya motar Hulux ce, dayar kuma babbar mota ce wadda aka lodo wa wake za ta Maiduguri. Har lokacin da mu ka isa wurin da safe, motar da ke dauke da waken ba ta daina cin wuta ba.”

Jami’in kungiyar Motocin Surufi na Maiduguri (NURTW), Malam Ali ya shaida wa wakilin mu cewa ba su da cikakken bayanin yawan mutanen da aka kashe.

An kai wannan hari kwana kadan bayan Babban Jafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Tukur Buratai ya yi shelar komawa Barno domin jan rundunar da za ta karasa Boko Haram kurmus.

Boko Haram sun sha tare matafiya kusa da Auno. Ana ganin cewa su na samun damar kai harin ne ta hanyar biyowa cikin kwararon wani burtali da ke kusa da garin Auno.

Idan ba a manta ba, Jihar Barno ta saka dokar zirga-zirga a fadin titinan jihar, banda na Maiduguri zuwa Damaturu.

Dukkan kokarin jin ta bakin Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya Sagir Musa, ya ci tura, domin bai amsa kira ko maida amsa ba.

Jihohin Barno da Yobe da wasu sassa na Adamawa na ci gaba da fuskantar hare-hare daga Boko Haram.

Share.

game da Author