Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kaduna Amina Baloni ta bayyana cewa an samu karin mutum biyar da suka kamu da cutar Covid-19 a jihar.
Amina ta ce mutum biyar din da suka kamu da cutar almajirai ne da aka dawo da su daga Kano.
Yanzu adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar a Kaduna sun kai mutum 9 a jihar.
Sannan kuma tuni har ma’aikatan kiwon lafiya sun fara farautar mutanen da suka yi cudanya da wadannan almajirai biyar domin killace su da yi musu gwajin cutar.
“Muna da wuraren yin gwajin cutar coronavirus guda biyu a jihar daya na cikin garin Kaduna dayan kuma a Zariya.
Daga nan sai tayi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin gujewa kamuwa da cutar domin kare kiwon lafiyar su.
Mutum 1532 na dauke da cutar a Najeriya, mutum 255 sun warke, 44 sun mutu.
Idan ba a manta ba ranar Litini Gwamnatin Kaduna ta kara kwana daya, bayan janye ranar Talata da ta yi ranar walwala a jihar.
Mutane a jihar za su rika yin walwala duk ranar Laraba da Asabar. Su garzaya Kasuwa su siya abinci sannan su koma gida.
Yin haka sassauci ne daga dokar da gwamnatin jihar ta saka na soke ranar Talata a matsayin ranar walwala a jihar.