WASIKAR KWANKWASO GA BUHARI: Ka tausaya wa Kanawa, a kara wuraren yin gwajin Coronavirus

0

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasika a bude, inda ya yi masa kira da babbar murya ya ceci al’ummar Kano daga yawan mace-macen da ake yi da kuma matsalar cutar Coronavirus.

Kwankwaso ya ce idan Buhari bai hanzarta ba, to ya na ji ya na gani al’ummar Kano za su rika faduwa su na mutuwa.

Kadan daga abin da wasikar ta kunsa, ya nemi Buhari ya gaggauta tausaya wa Kanawa, sannan ya kara kafa cibiyoyin gwajin cutar Coronavirus a Kano.

Hadiman Kwankwaso biyu, Aminu Gwarzo da Saifullah Hassan duk sun tabbatar da cewa Kwankwaso din ne ya rubuta wa Buhari wasikar, ba ta bogi ba ce.

Kwankwaso ya yi korafin yadda aikin gwajin cutar Coronavirus ya shiririce a hannun ‘yan shiririta a Kano.

Sannan kuma ya ce babu hadin kai da fahimtar juna tsakanin masu yaki da cutar Coronavirus a Kano da kuma na Hedikwata da ke Abuja.

Daga nan kuma ya hi magana a kan rashin yarda da rashin amanar da al’ummar Kano ba su bai wa gwamnatin jihar.

“Idan mu ka yi la’akari da irin yadda manyan jihar nan ke mutuwa a lokacin cutar Coronavirus, da kuma yadda ake sagegeduwa wajen gawajin a Kano, za mu iya cewa mai yiwuwa cutar ce musabbabin mutuwar su.

“A gaskiya a halin yanzu jihar Kano ba ta da wani kwamiti mai yaki da cutar Coronavirus. Kafin taswatsewar sa ma, ba kwamitin kitki ba ne, wani gungu ne kawai na ‘yan jagaliya, wadanda ba su da kwarewa kuma ba masanan fannin cutar ba ne.”

Kwankwaso ya yi bayanin cewa za irin yadda gwamnatin jihar ta rika gardamar mace-macen da ake yi da kuma yadda ta rika tankiya da Kwamitin Yaki da Coronavirus na Kasa tun farkon samun cutar a Kano, ya sa al’ummar Kano ba su amimce da bai wa gwamnatin jihar amana ba.

A kan haka, ya kori gwamnatin tarayya ta shigo tsamo-tsamo ta taimaki al’ummar Kano, kada ta bar harkar yaki da wannan annoba a hannun ‘yan jagaliya, wadanda ka iya barin rayukan dimbin al’umma ya salwanta, saboda siyasantar da lamarin.

Kwankwaso ya yi tsokaci kan irin kuncin da al’umma su ke ciki a Kano. Ya yi kira cewa ba kulle jama’a a gida kadai ne fa’ida ba. Sai an hada da tallafi, wanda ya ce gwamnatin tarayya ta shigo ciki, kada a bar lamarin a hannun wadanda za su saka siyasa a lamarin.

Share.

game da Author