Wani daga Kano ya yi dakon coronavirus zuwa Adamawa

0

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa mutum daya ya kamu da cutar COVID-19 a jihar.

Fintiri ya fadi haka wa manema labarai a garin Yola ranar Laraba.

Ya ce an gano cutar a jikin daya daga cikin mutum uku da aka yi wa gwajin cutar.

Fintiri ya ce Bincike ya nuna cewa mutumin da ya kamu da cutar matafiyi ne da ya shigo jihar daga jihar Kano.

Ya ce ma’aikatar kiwon lafiya sun fara yin bincike don gano duk wadanda suka yi cudanya da Wannan mutum domin a killace su, a yi musu gwajin cutar.

Idan ba a manta ba a ranar Talata ne Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan.

A sakamakon gwajin da ya fito ranar Talata, Jihar Legas ce kan gaba wajen yawn wadanda suka kamu da cutar, Sai kuma babban birnin Najeriya, Abuja.

Jihar Kano ma ta ci gaba da kawo maki mai yawa da har yanzu itace jiha ta uku da tafi yawan wadanda suka kamu.

Jihar Barno ma ta samu mutum dcaya cikin wadanda a ka fidda sakamakon gwajin su ranar Talata.

A bayanan da NCDC ta fitar ranar Talata, Legas ta samu karin mutum 59, Abuja 29, Kano 14, Katsina 3, Ogun 3, Bauchi 1, Barno 6, Ribas 1.

Yanzu mutum 782 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 197 sun warke, 25 sun mutu.

Share.

game da Author