Duka da hana sallolin jam’i da gwamnatin Kaduna ta yi, wasu masallatai na tara jama’a masu yawa suna sallar Jam’i musamman Magriba da Sallar Asuba.
Babban abinda ya mutane basu sani ba shine ba a hana salla a masallaci don nuna iko da karfin gwamnati bane, ana yin haka ne domin a kare al’umma daga yaduwar cutar Coronavirus da ke ci gaba da yaduwa a kasar nan har da jihar Kaduna.
Idan ka shiga Lunguna lunguna, akwai masallatai da mutane suke sallah a ciki batare da an san su ba. Za kaga an gwarmatsu, an cika tam ana sallah. Yin haka zai kara wa gwamnati nauyi ne na kula da mutane idan aka kamu da cutar coronavirus.
Unguwannin unguwan Dosa, Malali, Badarawa, U/Rimi duk zaka ga ire-iren wadannan masallatai da ake cunkoso da karya dokar gwamnati.
Haka a wasu jihohin Arewacin Najeriya, gwamnatoci na fama da matsalar karya doka.
Manyan malamai sun karantar kuma sun yi kira da a kaurace wa duk wani wuri da za a samu cunkosa domin kare kai daga kamuwa da yada cutar coronavirus. A kasar saudiyya da nan ne mahaifar, Annabin tsira, SAW ta dakatar da ire-iren wadannan cunkoso a wajen bauta domin dakile yaduwar cutar.
Yin taurin kai da nuna isa ba shine wai kana tsoron Allah ba. Tsoron Allah shine abi umarnin shugabanni, wadda ya hada da wadanda ke jagorantar mu da kuma wadanda suke karantar da mu addini.
Idan da mutane za su yi hakuri su kiyaye cudanya da cunkoso a tsakanin su da hakan ya fi zama alkahiri da yin da na sani. A hakura ayi sallah a gida, a ci gaba da rokon Allah, kamar yadda Kasashen musulunci na duniya suka yi don kiyaye mutanen su daga kamuwa da cutar.
A duba yadda cudanyar matafiya daga wasu jihohin kasar nan suka yada cutar zuwa wasu jihohi. Duk saboda yin taurin kai ne da nuna ba a isa a saka mutum ba.
A ci gaba da addu’o’i a wannan wata mai alfarma, Allah ya kawo mana Karshen wannan cuta.
Discussion about this post