TATTALIN ARZIKIN KASA: Najeriya ta rufta cikin mummunan halin da ba ta taba ruftawa a gwamnatocin baya ba – Osinbajo

0

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya fito gar-da-gar ya shaida wa ‘yan Najeriya cewa, kasar nan ta rufta cikin wani mummunan mawuyacin halin da ba ta taba samun kan ta a baya ba.

“Ranar wanka dai ba a boyon cibi. Ya zama tilas mu fito mu shaida wa Jama’a halin da kasar nan ta ke ciki a yanzu. Mun daina lissafin-dawakan-Rano. Domin mu na fuskantar wani gagarimin kalubalen da a tarihin kasar nan, babu wata gwamnati da ta taba ruftawa cikin irin wannan mawuyacin hali. Saboda haka tilas sai mun sauya fasalin tsarin tasarifin tattalin arzikin mu da kuma canja irin tunanin mu.”

Wannan bayani da ke sama shi ne wani yanki daga jawabin da Osinbajo ya yi a ranar Alhamis, wajen kaddamar da Kwamitin Hana Tattalin Arziki Durkushewa wanda Buhari ya kafa a ranar Litinin, da nufin sake fasalin tsarin tattalin Arziki sakamakon cutar Coronavirus a duniya da kuma faduwar fasashin danyen man fetur warwas a duniya.

Najeriya ta rufta cikin wasakeken ramin barazanar durkushewar tattalin arziki bayan cutar Coronavirus ta haddasa faduwar farashin danyen man fetur, daga dala 57 kowace ganga daya zuwa har kasa da dala 20.

Najeriya dai ta tsara kasafin kudin 2020 a kan farashin danyen man fetur dala 57 kowace ganga daya.

Dama kuma a farkon wannan makon Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ta ce Najeriya ba za ta iya aiwatar da ko da rabin alkawurran ayyukan da ke cikin kasafin kudi na shekarar 2020.

Sannan kuma Kyari, Shugaban Hukumar NNPC ya ce idan har farashin danyen man fetur ya sauka zuwa dala 22 a kan kowace ganga, to za ta daina hako mai har sai bayan annobar Coronavirus ta wuce.

A kan haka ne Buhari ya kafa Kwamitin Hana Tattalin Arziki Durkushewa, wanda aka dora wa alhakin fito da sabon fasali da salon tsarin tattalin arzikin da gwamnati za ta Yi amfani da shi a hau tudun-mun-tsira nan da shekaru uku masu zuwa.

Osinbajo ya ce Buhari na fatan wannan kwamiti duk rintsi zai fito da tsarin da zai hana dimbin jama’a raya ayyukan su. Sannan ya tabbatar da an kara samun ayyukan yi a cikin wannan mawuyacin halin da aka tunkara gadan-gadan.

Wasu daga cikin mambobin kwamitin da suka halarci taron, sun hada da Ministar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, na Kasuwanci da Bunkasa Zuba Jari, Niyi Adebayo, Ministan Kwadago, Chris Ngige, na Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, Ministar Ayyukan Jinkai, Sadiya Umar da Karamin Ministan Fetur, Timipre Sylva.

Akwai kuma Shugaban Hukumar NNPC, Mele Kyari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile.

Share.

game da Author