Farashin gangar danyen man fetur a Amurka da Canada ya fadi kasa warwas, ta kai kyauta ma ake neman wanda zai kwasa, amma an rasa.
A ranar Lahadi farashin ya fadi zuwa dala 12, ranar Litinin da yamma ya sake faduwa zuwa dala 3. Amma kafin wayewar garin Talata agogon GMT, sai da kwalin karan taba sigari ya fi gangar danyen man fetur daraja a kasuwar duniya.
Wannan mummunar karyewa da farashin ya yi dai bai taba yin kamar ta a tarihin samuwar danyen mai a duniya.
Mece Ce Gangar Danyen Mai: Gangar danyen mai wata rindimemiyar randa ce, wadda ake zuba danyen man fetur a cikin ta, ana fitar da shi kasashen duniya.
Lita Nawa Ke Yin Gangar Danyen Mai?: Gangar danyen mai na daidai da lita 159, wato daidai da jarkar yan-ga-ruwa guda 6 mai cin lita 25 kenan.
A yanzu dai duk wata kasar da ta hako danyen mai, to asara za ta yi, saboda ana kashe akalla dala 17 wajen dawainiyar hako kowace gangar danyen mai daya a Najeriya.
A Amurka dai an kai ana biyan dillalai su kwashe danyen man da ke jibge, domin idan ba a kwashe shi ba, to nan da watan Mayu za a nemi wurin tara danyen mai a rasa.
Tuni kamfanonin mai a Amurka sun fara daukar hayar manyan tankoki su na jibge danyen mai a ciki. Wannan ne ya sa farashin danyen man bai kai ko dala daya ba.
Wani karin dalilin faduwar man a lokacin Coronavirus din nan, shi ne masu hada-hadar danyen mai na ganin cewa asara ce su rika saye su na tule shi zuwa wani lokaci tare da rika biya masa ladar ajiya.
Maimakon haka, sai suka daina bukatar sa a yanzu, saboda ba shi da tasiri, tunda duk wasu injina da ababen hawa da masana’antu masu amfani da mai a duniya duk a tsaye su ke cak, saboda Coronavirus.
Najeriya: Matsala Goma Da Ashirin
Litinin da ta gabata zuwa Juma’a, danyen man Najeriya ya karye zuwa dala 12 duk ganga daya.
Manyan ‘yan tiredar danyen mai sun ce yanzu haka akwai danyen mai ganga milyan 10 jibge a Najeriya, na cikin watan Afrilu, da aka hako, amma an rasa mai saye.
Ana jin nan da watan Mayu za a kara samun wasu ganguna milyan 60 a kasa, tunda babu mai saye a duniya, saboda matsalar Coronavirus.
Masu hada-hadar danyen mai sun ce man Najeriya ya ci na sauran kasashe kwantai da kuma yawa tule a kasa babu mai saye, saboda kasuwannin mai a Turai sun yi cimbu.
Haka su ma masu hada-hadar mai ta hangar Tekun Atilantika da Arewa Maso Gabacin Ruwan Asiya sun karyewar kasuwar ta shafe su. Saboda a Turai ana neman masu sayen mai, amma an rasa.
Masana a jiya Litinin sun ce babu wanda zai iya kintace ko shaci-fadin lokacin da darajar farashin gangar danyen mai zai sake tashi a duniya, matsawar ba a kakkabe cutar Coronavirus a duniya ba.
Discussion about this post