TARZOMA: Yadda jami’an tsaro suka bindige ‘yan bursuna biyar cikin Kurkukun Kaduna

0

Sabanin yadda daga farko Jami’an Hukumar Gidajen Kurkuku suka kantara karya cewa babu wanda aka kashe a wurin tarzomar, PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kashe daurarru har biyar a tarzomar, wadda ta tashi cikin kurkukun Kaduna.

Sannan kuma PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa an yi wa Jami’an tsaro 16 rauni. Har yanzu kuma goma daga cikin su na kwance a wani asibiti da ba a bayyana sunan sa da inda ya ke a Kaduna ba. Amma an rigaya an sallami sauran shida din.

Tun a ranar Talata ce dai wasu daurarru a gidan kurkurun suka tayar da tarzoma, bisa zargin cewa wata mata da ke tsare ta kamu da cutar Coronavirus, har ma an garzaya da ita asibiti.

Kafin sannan kuma akwai tuburrewar umarnin da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya bayar, cewa a rage cunkoson gidajen Kurkuku a kasar nan. Aregbesola dai ya samu wannan umarni ne daga shawarar daga Kwamitin Shugaban Kasa mai Yaki da Coronavirus.

Yadda Tarzomar Ta Barke

Al’amarin ya faru bayan an kawo wata mata an tsare. Ba a dade ba sai ta fara rashin lafiyar da ke da alamun kamuwa da cutar Coronavirus.

Majiya a cikin kurkukun ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa daga baya sai labari ya cika gidan kurkukun cewa matar ta mutu a asibiti.

To dama kuma yawancin daurarrun duk su na cikin zaman jiran za a sallame su ne, saboda Kwamitin Shugaban Kasa ya ce a sallami wasu daurarru da dama, domin a rage cunkoson da ka iya haifar da Coronavirus.

Me zai faru, maimakon daurarru su ji an fara kiran sunayen su ana sallamar su, sai ma suka fahimci ana hana duk masu kai musu ziyara ko kai musu abinci daga gida shiga cikin kurkukun.

“Ganin haka sai hatsaniya ta kaure, har daurarrun suka fara yi wa Jami’an kurkukun sababi. To gayyato jami’an tsaro dauke da bindigogi daga waje, ya munanta tarzomar, domin bude wuta kawai suka yi.

PREMIUM TIMES ta tabbatar cewa wani wanda ake tuhuma da laifin kisa ne mai suna Hammed Abdullahi ne aka bindigewa. Sai kuma wani Lucky Ugokam da ake tuhuma da laifin fyade.

An kuma harbi wani mai suna Yahu Salisu a duwaiwai, daga bisani ya rasu.

Sauran mutane biyu kuwa, Ibrahim Abubakar da ake kira Lolo, shi da wani da aka yanke wa hukuncin kisa kisa mai suna Olochukwu Iche, an rika zabga musu azaba ce har ran su ya fita.

Rufa-rufar Jami’an Tsaro

Binciken PREMIUM TIMES ta karkashin kasa a kurkukun ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun gigice wajen kokarin yin rufa-rufa, domin kada a kama su day laifin kisan daurarrun.

Majiya ta shaida wa jaridar nan cewa an yi kokarin shafa wa wasu daurarru kashin kaji, aka ce su rubuta bayani a rubuce cewa su ke da laifi.

“Amma wani da ya ki amincewa, cewa ya yi sai dai a kashe shi, amma shi ba zai dauki laifi da bai yi ba, ya ce ya yi.”

Wata majiya kuma ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa lokacin da aka yi tarzomar ba a karya makullan kofa ko daya ba.

“Amma washegari sai mu ka ga jami’an kurkukun sun balle wasu makullai da kofofi, domin su kafa shaidar-zir cewa wai kokarin tserewa daurarrun suka yi, har suka balle kofofin dakunan su.”

Sanann kuma majiyar ta kara da cewa, “mun ga an kawo wasu da dare lafiyar su kalau. Amma washegari sai mu ka ga kowanen su da bandeji. Su za a nuna a ce jami’an tsaro ne da aka ji wa rauni.

Da PREMIUM TIMES ta kira kakakin gidan kurkukun kasar nan, Austin Njoku, sai ya karyata cewa an yi kisa. Ya ce ko harbi ma ba a yi ba, kuma ya na kan hanyar zuwa Kaduna domin ganewa da idon sa.

Daga baya ranar Juma’a da aka bayyana masa hujjojin cewa an kisa, sai ya nuna cewa ya na jiran ogan su kwata-kwata ya fitar da bayani tukunna.

Daga baya ya tabbatar da bayanan PREMIUM TIMES tare da cewa an ji wa jami’ai 16 rauni.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka shiga rikicin tsamo-tsamo, domin kare hakkin daurarru. Sun kuma yi tir da abin da jami’an tsaron suka yi musu.

Share.

game da Author