Tambayoyi da amsoshi 9 kan cutar coronavirus

0

Mutane 219 sun kamu da cutar coronavirus, an sallami mutane 25 da suka warke daga cutar sannan 4 sun mutu a Najeriya.

Akwai muhimman tambayoyi da mutane ke ke neman amsarsu da muke samo muku amsoshin su.

1. Tambaya: Ya ake kamuwa da cutar coronavirus?

Amsa: Idan yawun mai dauke da cutar ya taba ka. ko kuma Idan mai dauke da cutar ya yi atishawa ko tari kusa. sannan kuma da taba wuraren da mai dauke da cutar ya ta da abubuwan da ya tattaba. A takaice dai wuraren da basu da tsafta duk suna iya sa a akmu da cutar. Yin Musabaha da wanda ke dauke da cutar.

2.Tambaya: Shin za a iya kamuwa da cutar ta hanyar cudanya da dabbobi?

Ansa: Babu binciken da ya tabbatar cewa cudanya da dabbobi kamar su kare, mage na iya sa a kamu da cutar.

3. Tambaya: Wasu hanyoyi ne za a kiyaye don kauce wa kamuwa da cutar?

Amsa: Yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu na tsawon sakan 20 ko kuma yawaita amfani da man tsaftace hannu wato ‘Hand sanitizer’.

A daina zama kusa da mutanen dake fama da mura da rage yawan taba fuska. Sannan a gaggauta zuwa asibiti idan an kamu da tari, rashin iya mumfashi ko Zazzabi. Sanna a nesanta kai daga mutane idan aka ga alamun kamuwa da wannan cuta.

4. Tambaya: Shin cutar na iya kama kuwa?

Amsa: Kowa na iya kamuwa da cutar babu babba ko yaro. Sannan tsofaffi da wadanda ke fama da wasu cututtuka kamar asthma, ciwon siga, cututtuka dake kama zuciya da wadanda ba su da karfin garkuwan jiki sun fi saurin kamuwa da cutar.

5. Tambaya: Wani irin man tsaftace hannu ya kamata arika amfani da shi

Amsa: Man da ke kunshe da sinadarin Alkohol akalla kashi 60% na na ruwan sinadarin.

6. Tambaya: Shin ko akwai maganin warkar da coronavirus?

Amsa: Har yanzu ba a samo maganin warkar da cutar coronavirus ba. Ana nan ana ci gaba da yin bincike gama da haka.

7. Tambaya: Minti nawa ya kamata a dauka wajen warke hannu?

Amsa: Akalla sakan 20 ya kamata a dauka ana wanke hannu. Sannan a wanke hannu da ruwa da sabulu.

8. Tambaya: Me nene marabar Mura da coronavirus?

Amsa: Akwai bambanci tsakanin coronavirus da mura. Kowanne yana a matsayin sa da bam. Sai dai alamun mura ne za a yi fama da idan aka kamu da cutar coronavirus.

9. Tambaya: Shin ko ana iya kamuwa da coronavirus lokacin zafi ko lokacin sanyi?

Amsa: Coronavirus na kama mutum lokacin zafi da sanyi. A rage mu’amala da ruwan sanyi.

Share.

game da Author