Birnin Zazzau gari ne da Allah ya yi ma baiwa da abubuwa da dama na alheri da suka hada da: manyan malaman addini da na boko manyan makarantu da ma’ikatu, arzikin hazikan jamaa masu sanao’i daban daban don samun abin sawa a bakin salati.
Saidai kash! A yayin da wasu ke faman neman hanyoyi don tsaftace sana’o’in su, wasu kuwa kara tabarbarashi sukeyi wanda hakan ke cutar da al’umma, musamman yara da matasa wadanda sune ake dubi gare su a matsayin ginshikai kuma manyan gobe.
Sanar saida magungunan gargajiya sana’a ce mai asali ,wanda kusan a ce duk fadin duniyan nan ba wanda zai ce bai taba mu’amala da wandannan magunguna ba.
To amma. yadda wadansu masu baiwar hadawa da sayar da wadannan magunguna ke tafaiyar da tallace- tallacen su abun gwanin ban takaici. Mutum ne zaka ga ya manyanta ga suffar kamala amma sai kaji yana bude baki yana furta kalaman batsa iri ko ajikinsa wai da sunan yana tallar hajarsa.
Abin takaici basu dubawa cewa kalamansu nada illa ga al’umma musamma yara da ke kai kawo a irin wuraren da ake wannan tallace-tallacen wanda ya hada da kasuwanne da bakin tituna, cikin Anguwanni da sauransu. Wani Karin haushi shine yadda zaka ji wasu yara suna maimaita wadannan kalamai ba tare da ma sun san me suke furtawa ba.
Karin abun takaici shine manyan mutane suna ji, kuma a gaban su ake wannan tallar. amma kuma ba alamar suna nuna bacin ransu ko tsawatarwa,don kuwa kullum abin karuwa yakeyi.
A sanin mu,kowacce sana’a tana da shuwagabanni a matakai daban-daban. Asali ma a dokar tallace-tallce ta kowane kafa ba a yarda da kalamai ko hotunan batsa ba,wannan kuma zamu iya lura in muka yi dubi da kafafen yada labarai na Jaridu, Talabijin da Radiyo.
Abin tambaya anan shine: an yarda da kalamun batsa ne a kungiyar masu tallar maganin gargajiyar jihar Kaduna ne (duba da yadda a kasan mu da ilimin addini?);Shin shuwagabanin kungiyar na sa’ido akan yadda mambobin ta ke aiwatar da ayyukan su musamman talace-tallace kuwa?;
Ba dokar ladaftarwa in mambobi sun kauce hanya? Me iyayen kasa sukayi ko suke don kauda wannan matakalar bata tarbiyar alummarsu?
A dai shekarun baya da suka wuce mutanen Zariya sunsan wani mai tallar maganin gargajiya mai taken: ‘giggirka manaja’,amma basu san shi da kalaman batsa ba,yakan wuce ta anguwowi yana tallarsa a mota ba cuta ba cutarwa.
Mafita ko shawari ga dukannin al’umma, musamman gwamnati:
1. A saka doka mai karfi kuma mai aiwatuwa don dakile irin wannan tallar ta batsa da yayi yawa a garin zariya.
2. A saka iyayen kasa tsundum aciki (tun daga kan mai anguwa zuwa sarakuna)wajen yakar wannan mummunar dabi’ar da kuma gurfanar da masu yin haka gaban hukuma.
3. Mutanen Anguwa da masu zama a bakin tituna su runka hana irin masu wannan batsar tsayawa a tituna ko shiga anguwanni,in dai kuma ba batsar kake so ba. Wannan yana cikin hakkin zaman bakin titi.
Ko kadan ba inkarin maganin gargajiya akeyi ba, asali ma duk magungunan bature daga na gargajiya ne,kuma tabbas hanyace ta samun kudi din rufa ma kai asiri. Amma akwai bukatar tankade da rairaya,a tsaftace yadda suke talla,domin kuwa mudin ba a ja musu birki ba ,to tabarbarewar tarbiyya a zariya yanzu aka fara!