Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta gargadi mutane cewa su daina daura takunkumin rufe baki da hanci, sai idan sun kamu da cutar Coronavirus ko kuma su na kusa da marar Lafiya.
Babban Daraktan Lafiya Mike Ryan ya yi wannan gargadin a hedikwatar WHO a Geneva, babban birnin Switzerland, ranar Litinin, kamar yadda CNN ta ruwaito.
“Babu wata hujja mai tabbatar da cewa idan mutane su na kakaba takunkumin rufe hanci da fuska, ba za su kamu da cutar ba.
“Akwai ma yiwuwar kakaba ta a baki da hanci ba daidai ba ka iya haddasa wa mutum yiwuwar kamuwa da cutar.”
Kafin nan sai da WHO ta yi kukan cewa takunkumin ya yi karanci a duniya ga wadanda su ne suka wajaba su na makala shi. Wato jami’an lafiya masu kula da marasa lafiya.
Hakan ya faru ne yadda a duniya aka rika fagamniyar neman sa ido-rufe ana saye ana daurawa a hanci da baki, domin gudun kamuwa da cutar Coronavirus.
Ryan ya ce karancin da takunkumin ya yi a duniya ya jefa rayuwar jami’an kula da lafiya cikin hadarin gaske.
“A zaman yanzu wadanda ke kan barazanar kamuwa da wannan cuta, su ne jami’an lafiya masu aiki ba dare ba rana wajen kula da masu cutar da kuma ayyukan dakile cutar.
“Babban bala’i ne a ce ga jami’an kula da ayyukan hana Coronavirus yaduwa, amma kuma ba su da takunkumin daurawa a baki da hancin su.”
Annobar Coronavirus ta kashe likitoci da jami’an lafiya da dama a duniya. Sama da likitoci 3,000 ne suka kamu da cutar a Chana, sannan kuma likitoci 60 cutar ta kashe a Italy.
A wasu kasashe da dama, masana’antu na ci gaba da dinka takunkumin domin taimaka wa gwamnati kokarin yankin dakile Coronavirus.
Sai dai kuma a Najeriya tuni farashin takunkumin ya wuce hankali da kuma aljihun talaka.
Kafin bullowar cutar Coronavirus, ana sayar da kowane takunkumi daya a kan naira 50 a Abuja. Amma da annobar Coronavirus ta shigo, farashin sa ya kai naira 500.
A wasu garuruwan da ke nesa da Abuja ana sayar da shi naira 200. Da yawan matasa masu sayar da kayayyaki a mahadar titina ko a bakin danja inda motoci ke tsayawa, sun yi watsi da sana’o’in su na asali su ka koma sayar da takunkumi zalla.
Duk da wasun su sun shaida wa PRWMIUM TIMES HAUSA cewa su ma da tsada su ke saro shi, duk da haka dai bincike ya nuna cewa idan suka sayar da kwaya daya kan naira 500, to a kowane daya su na nunka riba.
Ba a sani ba ko alkadarin kasuwar takunkumin za ta karye, tun daga yanzu da WHO ta yi gargadi kan masu amfani da shi ga su nan kan hanya.
Discussion about this post