Shugabannin Majalisar Tarayya da ta Dattawa, sun nemi a yi taka-tsantsan da kuma tsantseni wajen kashe makudan kudaden gudummawar da aka yi wa alkawarin za a bayar ko ko aka bayar domin yakin Coronavirus a kasar nan.
Mutane da dama sun yi sanarwar bayar da tallafin kudade da kayayyaki na bilyoyin nairori.
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa da Femi Gbajabiamila Kakakin Majalisar Tarayya, sun yi wannan kira ne bayan sun hana da Buhari.
Idan ba a manta ba, cikin makon jiya sun yi tir da tsarin da Gwamnatin Tarayya ta bi wajen rabon kudaden tallafin rage radadin kunci.
A Sauya Fasalin Yaki Da Talauci a Najeriya -Lawan
Da ya ke magana da manema labarai, Lawal ya ce kamata ya yi a ce a cikin asusun bai-daya, wato TSA za a rika ajiye kudaden. Sannan kuma a nada musu kwamitin kula da yadda ake kashe su.”
Sun kuma yi kira a sake fasalin rabon kudaden, domin su rika zuwa wurin marasa galihun da aka ware kudaden domin su.
“Na kuma yi amanna cewa akwai bukatar a sake fasali tare da kafa dokar yadda za a rika rage kuncin talauci ga dimbin jama’a a kasar nan.”
A Saukake Biyan Kudin Wuta a Lokacin Zaman Gida
Gbajabiamila ya ce sun tattauna batun a sahale wa ‘yan Najeriya biyan kudin wuta tsawon Watanni biyu, saboda zaman da suke faman yi a gida sanadiyyar Coronavirus.
“Mun tattauna batun sauke wa jama’a kudin wuta a wannan lokacin zaman gida. Mun nuna masa jama’a za su samu rangwame sosai, saboda zaune su ke a gida, babu wani aiki da su ke yi.
“Mun kuma gamsu cewa ya fahimce mu. Nan ba da dadewa ba za a ji bayani daga gare shi, idan ya gana da masu ruwa da tsaki a fannin lantarki.
“Mun san akwai matsaloli tartare da kamfanonin DisCos masu raba wutar lantarki. Amma dai abu mafi muhimmanci a gare mu, shi ne saukake wa ‘yan Najeriya kuncin da suke ciki a wannan lokaci na zaman-dirshan a gida.” Inji Gbajabiamila.
Discussion about this post